Kotun ƙoli ta umarci lauyoyi su loda takardun shari’o’i kafin zaman Satumba

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kotun ƙolin Nijeriya ta umarci lauyoyin da ke kula da ƙarar daukaka ƙara da kuma buƙatun da aka tsara za a saurara tsakanin watan Satumba zuwa Disambar 2026 da su loda dukkan takardun shari’o’insu ta hanyar Tsarin Gudanar da Shari’o’in Nijeriya (Nigerian Case Management System – NCMS), daidai da tanadin Doka ta 10(1) na Jagororin Aiki na Kotun ƙoli na shekarar 2026.

Wannan umarni na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Babban Magatakardan Kotun ƙoli, Kabir E. Akanbi, ya aikewa da News Point Nigeria, inda ya buƙaci lauyoyi su duba jerin shari’o’in da aka tsara za a saurara a wannan lokaci.

Lauyoyi na iya samun damar ganin jerin shari’o’in ta hanyar ziyartar shafin intanet na Kotun ƙoli, sannan su shiga sashen Litigation, su zaɓi Nigerian Case Management System (NCMS), inda aka sanya jadawalin sauraron ƙarar daukaka ƙara da sauran buƙatu domin saukewa.

A cewar Kotun ƙolin, ana sa ran lauyoyi za su loda dukkan takardun da suka riga suka shigar a cikin shari’o’insu, ciki har da Takardun Daukaka ƙara (Records of Appeal), Takardun Hujjoji (Briefs of Argument), buƙatun da har yanzu ba a yanke musu hukunci ba, da kuma duk wasu takardun shari’a masu alaƙa, aƙalla kwanaki 30 kafin ranar sauraron shari’ar.

Kotun ta bayyana cewa wannan mataki na da nufin tabbatar da bin ƙa’idojin Jagororin Aiki na Kotun ƙoli, inganta yadda tsarin NCMS ke aiki, da kuma taimakawa wajen hanzarta yanke hukunci da gudanar da shari’o’i cikin sauƙi da inganci.

Kotun ƙolin ta kuma yi kira ga dukkan lauyoyin da ke da shari’o’in da aka tsara za a saurara a cikin wannan lokaci da su bi wannan umarni ba tare da gazawa ba.

By ukarofi

Leave a Reply