Ribadu ya karɓi baƙuncin babban jami’in diflomasiyyar Amurka, Garcia, kan haɗin gwiwar tsaro

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mai Bai wa Shugaban ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu, ya gudanar da wata ganawa da wata babbar tawagar gwamnatin Amurka ƙarƙashin jagorancin Frank Garcia, sabon Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mai Kula da Harkokin Afirka, domin ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka.

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa taron, wanda aka gudanar a Abuja, shi ne ziyarar aiki ta farko da Garcia ya kai Nijeriya tun bayan da ya karɓi muƙaminsa a ranar 1 ga Yuni, 2026, kuma yana cikin wata babbar ziyarar diflomasiyya da yake yi a ƙasashen Yammacin Afirka.

Ziyarar Garcia a yankin, wadda za ta gudana daga ranar 11 zuwa 18 ga Yuli, ta kuma haɗa da ƙasashen Côte d’Iɓoire da Mali.

Bayan ganawar, Ribadu ya bayyana cewa tattaunawar ta mayar da hankali ne kan ƙarfafa dangantakar da ta daɗe tsakanin Nijeriya da Amurka, musamman a fannin haɗin gwiwar tsaro.

A cewarsa, ƙasashen biyu sun yi nazari kan ayyukan da ake gudanarwa a ƙarƙashin Kwamitin Haɗin Gwiwa na Nijeriya da Amurka tare da duba sabbin hanyoyin faɗaɗa haɗin kai wajen tunkarar matsalolin tsaro da suka shafi ɓangarorin biyu.

Ya ƙara da cewa tattaunawar ta sake jaddada aniyar gwamnatocin ƙasashen biyu na ci gaba da tattaunawa da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa wajen magance batutuwan da suke da muradun bai ɗaya a kansu.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na ɗ, Ribadu ya ce: “A ƙoƙarin ci gaba da bunƙasa nasarorin da muka samu a haɗin gwiwarmu da Amurka, na karɓi baƙuncin wata babbar tawaga ƙarƙashin jagorancin sabon Mataimakin Sakataren Harkokin Afirka, Frank Garcia, a ziyararsa ta farko zuwa Nijeriya tun bayan da ya karɓi muƙaminsa.”

Ya ƙara da cewa: “Ganawata da su ta ƙara ƙarfafa dangantaka mai ɗorewa tsakanin Nijeriya da Amurka, tare da duba ci gaban da aka samu a ƙarƙashin Kwamitin Haɗin Gwiwa, da kuma sake tabbatar da aniyarmu ta zurfafa tattaunawa, haɗin kai da fifita batutuwan tsaro da suke da muhimmanci ga ƙasashen biyu.”

Garcia na zuwa da gogewa mai yawa a fannin tsaro da harkokin leƙen asiri zuwa sabon muƙaminsa na diflomasiyya.

Kafin shiga Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, ya yi kusan shekaru talatin yana aiki a Rundunar Sojin Ruwa ta Amurka, sannan daga baya ya yi aiki a matsayin babban mai ba shugaban Kwamitin Dindindin na Majalisar Wakilan Amurka Kan Harkokin Leƙen Asiri shawara.

Haka kuma, ya taɓa zama Daraktan Ma’aikata na Kwamitin Leƙen Asirin Tsaro da Tsarin Kula da Harkokin Leƙen Asiri na Sararin Samaniya.

Naɗin Garcia ya cike wani muhimmin gurbi na diflomasiyya da ya shafe sama da shekara guda babu wanda ya riƙe shi, inda jami’an riƙon ƙwarya suka kasance suna tafiyar da harkokin ofishin.

Ziyararsa a Nijeriya na nuna ci gaba da mayar da hankali da gwamnatin Amurka ke yi ga ƙasashen Yammacin Afirka a kan batutuwan da suka shafi tsaro, haɗin gwiwar leƙen asiri da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin.

By ukarofi

Leave a Reply