ADC ta zaɓi Dr Zagi a matsayin mataimakin ɗan takarar gwamnan Kebbi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Jam’iyyar ADC a Jihar Kebbi ta amince da ɗaukar Dakta Musa M Zagi a matsayin mataimakin ɗan takarar gwamnan jihar a zaɓen 2027 idan Allah ya kai mu.

Wannan yana ƙunshe ne a cikin takarda mai ɗauke da sa hannun mataimakin sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar ADC ta Jihar Kebbi Injiniya Abubakar Atiku Musa ranar Juma’ar nan.

Takardar, bayan taya shi murna ta kuma yi fatan Allah ya ba shi ikon sauke nauyin da Allah ya ɗora masa da fatan Allah ya bai wa jam’iyyar ADC nasara a dukkan matakan kujerun tun daga ƙananan hukumomi zuwa na ƙasa.

By ukarofi

Leave a Reply