Sojoji sun kama wanda ake zargin ɗan ISIS ne daga ƙasar waje a Borno

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sojojin Nijeriya sun kama wani mutum da ake zargin mamba ne na ƙungiyar ISIS, wanda ake kyautata zaton ɗan ƙasar Moroko ne, a yankin Cross Kauwa da ke ƙaramar hukumar Kukawa a Jihar Borno.

Majiyoyin tsaro sun shaida wa jaridar Zagazola Makama cewa an kama mutumin ne bayan da sojoji suka dakile wani harin ta’addanci da aka kai a Cross Kauwa, lamarin da ya tilasta wa ‘yan ta’addar tserewa tare da barin wasu kayayyakinsu a wurin.

Bayan harin, sojoji sun fara bincike da kuma farautar ‘yan ta’addar a hanyoyin da suka bi wajen tserewa.

A yayin wannan aiki da aka gudanar ranar Litinin, sojojin sun ƙwato wasu muhimman kayan aiki da suka haɗa da na’urorin sadarwa masu amfani da mitar HF (High Freƙuency), waɗanda ake amfani da su wajen sadarwa da gudanar da ayyukan ƙungiyar.

Rahoton ya ce bayanan da aka samo daga waɗannan kayan aiki sun taimaka wa jami’an tsaro wajen faɗaɗa bincikensu har zuwa yankunan tsibiran Tafkin Chadi da kuma ƙaramar Hukumar Abadam, inda suka kama wannan mutumin da ake zargin ɗan ƙasar Moroko ne kuma yana da alaƙa da ƙungiyar ISIS.

Majiyoyin soji sun bayyana cewa tun da fari ana bibiyar mutumin ne bayan wani bincike da aka gudanar tare da haɗin gwiwar ƙasashen waje kan wasu bidiyoyi da aka samo daga wata kyamarar bidiyo da aka ƙwato bayan harin Cross Kauwa.

An ce kyamarar ta wani mai ɗaukar bidiyon ‘yan ta’adda ce wanda aka kashe yayin harin.

By ukarofi

Leave a Reply