Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mataimakin Shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya bayyana yadda ya zubar da hawaye lokacin da ya kai ziyara ga marigayi tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a wani asibiti da ke birnin London a shekarar da ta gabata, yayin da yake kallon yadda rayuwar tsohon shugaban ke ci gaba da dusashewa.
Rahoton News Point Nigeria ya ce Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin tarukan tunawa da cikar shekara guda da rasuwar Buhari, inda ya bayyana ziyarar da ya kai wa marigayin a asibitin London a matsayin ɗaya daga cikin lokutan da suka fi tayar masa da hankali a rayuwarsa.
A cewar Mataimakin Shugaban ƙasar, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne da kansa ya umurce shi da ya je London bayan samun rahotannin cewa lafiyar Buhari ta tsananta.
Shugaba Tinubu ya ce masa: “Kashim, yanzu na samu labarin cewa Shugaba Muhammadu Buhari ba shi da lafiya a London. Don Allah ka tafi can ka gano abin da ke faruwa, kuma ka tabbatar babu abin da yake buƙata da ya rasa.”
Shettima ya bayyana cewa abin da ya gani a asibitin ya girgiza shi matuƙa.
“Na fito daga ɗakin kula da marasa lafiya masu buƙatar kulawa ta musamman (ICU) idanuna cike da hawaye, inda na tarar da Zara da Yusuf, ‘ya’yan Buhari, a bakin ƙofar ɗakin. Wani lokaci ne mai raɗaɗi da tausayi sosai,” in ji Shettima.
Ya ƙara da cewa rakiyar gawar Buhari daga London zuwa Nijeriya domin yi masa jana’iza na daga cikin manyan darajojin da ya samu a rayuwarsa.
Daga bisani an dawo da gawar marigayin gida Nijeriya, inda aka yi masa jana’iza tare da binne shi a garinsu na Daura da ke Jihar Katsina.
Ayyukan tunawa da Buhari sun gudana ne a Abuja tare da halartar iyalansa, abokan siyasa, tsofaffin abokan aikinsa na soja da kuma waɗanda suka yi aiki ƙarƙashinsa.
Shugaba Tinubu ne ya jagoranci manyan baƙin da suka halarci taron, wanda ya samu halartar tsohon Shugaban ƙasa na mulkin soja Janar Yakubu Gowon, shugabannin Majalisar Tarayya, gwamnoni, sarakunan gargajiya da jami’an diflomasiyya.
Da yake wakiltar Shugaba Tinubu a wajen taron, Shettima ya gabatar da muhimmin jawabi tare da isar da saƙonnin ta’aziyya da yabon marigayin.
A saƙonsa, Shugaba Tinubu ya tabbatar wa iyalan Buhari cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da kasancewa tare da su a wannan lokaci na jimami.
Da yake jawabi ga tsohuwar Uwargidan Shugaban ƙasa, Hajiya Aisha Buhari, da sauran iyalanta, Tinubu ya ce: “Na san kun fuskanci wani lokaci mai cike da baƙin ciki da jimami. Ina tabbatar muku cewa ƙasa da wannan gwamnati za su ci gaba da kasancewa tare da ku yanzu da kuma nan gaba.”
Ya ƙara da cewa gwamnati za ta ci gaba da yi wa iyalan addu’a tare da roƙon Allah Madaukakin Sarki ya ba su haƙuri da juriya.
Da yake tuna alaƙarsa da Buhari a siyasa, Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin abokin tafiya a doguwar tafiyar siyasa da ci gaban ƙasa.
“Ya ba da duk abin da yake da shi domin wannan ƙasa ba tare da wata shakka ba. Ya yi hidima da jajircewa, da ƙwarin gwiwa da kuma kishin ƙasa na gaskiya,” inji Tinubu.
Shugaban ya kuma yabawa Buhari saboda yadda ya ci gaba da samun ƙauna da amincewar talakawan Nijeriya ko bayan barinsa mulki.
“Yawanci mulki kan sa shugabanni su rasa ƙaunar jama’a, amma bayan Buhari ya sauka daga mulki, amincewar da jama’a suke da shi ba ta gushe ba. Har bayan ya koma rayuwar sirri, jama’a sun ci gaba da ƙaunarsa,” in ji Tinubu.
Kafin ya karanta cikakken jawabin shugaban ƙasa, Shettima ya yi ɗan tsokaci kan yadda Tinubu ke nuna aminci ga abokansa, inda ya sake tuna yadda shugaban ya tura shi London domin duba lafiyar Buhari.
Tinubu ya kuma buƙaci abokai, almajirai da masu ruwa da tsaki da su ci gaba da riƙe kyawawan dabi’un da Buhari ya bari a matsayin gadonsa.
“Nauyin da ya rataya a wuyanmu shi ne ci gaba da ɗaukar kyawawan dabi’un da ya bari, kamar gaskiya, sauƙin kai da kuma ladabi,” in ji shugaban.
A nasa jawabin, tsohon Shugaban ƙasa Janar Yakubu Gowon ya bayyana Buhari a matsayin jarumin soja wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare haɗin kan Nijeriya.
Gowon ya kuma yaba wa dangantakar siyasa tsakanin Buhari da Tinubu, yana mai cewa marigayin ya mayar wa Tinubu alherin da ya yi masa ta hanyar mara masa baya domin ya zama shugaban ƙasa.
“Ya tsaya tsayin daka wajen ganin Tinubu ya zama shugaban ƙasa domin ya ci gaba da yi wa Nijeriya hidima,” inji Gowon.
Shi ma Gwamnan Jihar Katsina, Dakta Dikko Umaru Radda, ya bayyana Buhari a matsayin “alkiblar ɗabi’a” ta jihar Katsina da kuma shugaba mai gaskiya wanda ya zama abin koyi a aikin gwamnati.
Ta bakin Mataimakinsa, Malam Faruk Lawal Jobe, gwamnan ya ce rasuwar Buhari ta haifar da babban gibi, duk da cewa al’ummar Katsina na ci gaba da alfahari da gudummawar da ya bayar ga ƙasa.
Ya ce: “A nan Katsina, Buhari ya fi zama tsohon shugaban ƙasa kawai. Ya kasance ɗanmu abin alfahari da kuma jagoranmu na ɗabi’a. Bai taɓa mantawa da asalinsa ba.”
Radda ya ce duk da nasarorin da Buhari ya samu a fannonin ababen more rayuwa, layukan dogo, noma da shirye-shiryen jin ƙai, babban abin da ya bari shi ne misalin shugabanci mai tawali’u da sauƙin kai.
Ya kuma yi kira ga ‘yan siyasa da su rungumi ƙa’idodin rayuwar Buhari maimakon takaita girmamawarsa ga jawabai da bukukuwan tunawa kawai.
“Babbar hanyar girmama Buhari ita ce rungumar gaskiya, adalci, hidimar jama’a da haɗin kan ƙasa da ya rayu a kansu,” inji Raɗɗa.
Daga cikin manyan mutanen da suka halarci taron akwai gwamnonin jihohin Borno, Bauchi, Ogun, Lagos da Jigawa, da kuma Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziƙi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu.
Har ila yau, tsofaffin gwamnoni, ministoci, shugabannin APC na ƙasa da tsofaffin manyan jami’an gwamnati da dama sun halarci taron.
A nasa jawabin, tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma shugaban kwamitin shirya taron, Boss Mustapha, ya sanar da cewa iyalan Buhari na shirin kafa gidauniyar Muhammadu Buhari Foundation and Centre tare da wallafa wasu muhimman takardu domin adana tarihin rayuwar marigayin da gudummawar da ya bayar ga Nijeriya.
“Wannan rana ba wai kawai tuna rasuwar tsohon shugaban ƙasa ba ce, lokaci ne na tunawa da rayuwar hidima da sadaukarwa da ya yi wa Nijeriya,” inji Mustapha.
