Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Iyayen ɗaliban da aka sace daga Makarantar Firamare da Sakandiren Mussa da ke ƙaramar Hukumar Askira-Uba a jihar Borno sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ƙara ƙaimi wajen ceto ’ya’yansu, suna masu cewa suna jin kamar an yi watsi da su watanni biyu bayan aukuwar lamarin.
Rahoton Blueprint Manhaja ya bayyana cewa wannan kira ya zo ne ƙasa da sa’o’i 48 bayan jami’an tsaro sun samu nasarar ceto malamai da daliban da aka sace daga makarantu uku a ƙaramar Hukumar Oriire da ke jihar Oyo.
An sace mutanen a jihohin Borno da Oyo ne a rana guda, wato ranar 15 ga Mayu, 2026.
Fiye da ɗalibai da malamai 40, ciki har da yara masu shekaru biyu kacal, aka yi garkuwa da su daga makarantar Mussa.
Har zuwa yanzu babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin harin, yayin da iyalan waɗanda abin ya shafa suka ce ba su samu wani saƙo ko bayani kan inda ’ya’yansu suke ba.
Da yake magana da wannan jarida, shugaban kwamitin iyaye, Malam Ishaku Suya, ya ce al’ummar yankin na ci gaba da rayuwa cikin alhini da rashin tabbas tun bayan aukuwar lamarin.
A cewarsa, jami’in gwamnati guda ɗaya tilo da ya kai ziyara ga iyalan bayan sace yaran shi ne Kwamishinan Ilimi na jihar Borno, wanda ya tabbatar musu cewa ana ƙoƙarin ceto waɗanda aka sace.
“Tun daga lokacin ba mu sake jin komai ba. Mun yi farin ciki da jin cewa an ceto dalibai da malaman Oyo, amma tamkar an manta da namu yaran ne,” inji Suya.
Ya roƙi Gwamnatin Tarayya da ta nuna irin ƙwazo da gaggawar da ta nuna wajen ceto daliban Oyo domin ganin an kuɓutar da yaran Borno da aka sace.
“Mu ma ’yan Nijeriya ne. Muna roƙon gwamnati da ta nuna irin wannan jajircewa da hanzari wajen ceto ’ya’yanmu,” ya ƙara da cewa.
ɗaya daga cikin iyayen, Sale Buba, ya ce rashin sanin halin da yaran suke ciki ya jefa iyalai cikin damuwa da tashin hankali.
“Ba mu san inda yaranmu suke ba ko irin yanayin da suke ciki. Yayin da aka yi ƙoƙari wajen ceto waɗanda aka sace a Oyo, babu wanda yake magana kan namu,” in ji shi.
Wani mahaifi, Ishaku Joe, ya ce shiru da aka yi kan lamarin ya ƙara tsananta wa iyalan radadin da suke ciki.
“Ba mu san ko suna raye ba, ko suna samun abinci, ko kuma irin halin da suke ciki a cikin daji. Muna jin kamar an yi watsi da mu,” in ji ta.
Shi ma wani mahaifi mai suna Malam James ya nuna takaicinsa, yana mai cewa duk da cewa kundin tsarin mulkin ƙasa ya ɗora wa gwamnati alhakin kare dukkan ’yan ƙasa, iyalan suna jin an bar su a lokacin da suka fi buƙatar taimako.
A halin yanzu, wata haɗakar matasa da ɗalibai ta gudanar da zanga-zangar lumana a Maiduguri domin nuna damuwa kan taɓarɓarewar tsaro tare da neman a ceto daliban da aka sace cikin gaggawa.
Masu zanga-zangar sun ɗauki alluna masu ɗauke da saƙonni daban-daban, inda suka buƙaci Gwamnatin Tarayya ta yi amfani da dukkan hanyoyin da take da su wajen ceto yaran da aka sace daga Mussa, Lassa da sauran yankunan da abin ya shafa.
Da yake jawabi ga masu zanga-zangar a yankin Post Office da ke Maiduguri, jagoran zanga-zangar, Suleiman Muhammed, ya yaba wa jami’an tsaro bisa nasarar da suka samu wajen ceto dalibai da malaman Oyo, amma ya buƙaci gwamnati ta yi irin wannan ƙoƙari a Borno.
“Mun yi imanin cewa gwamnati ba za ta nuna bambanci tsakanin wani yanki da wani ba. Irin ƙudurin da aka nuna a Oyo ya kamata a nuna shi wajen ceto yaran da har yanzu suke hannun masu garkuwa da mutane a Borno,” inji shi.
Muhammed ya kuma buƙaci gwamnati ta samar da ayyukan yi da damar tattalin arziki ga matasa a matsayin wani mataki na rage laifuka da matsalar tsaro.
Ya kuma yi gargadi kan biyan kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutane, yana mai cewa hakan na ƙara ƙarfafa masu aikata laifuka tare da ƙara yawan sace-sacen mutane.
Wani daga cikin masu zanga-zangar, Muhammed Mustapha, ya tambayi dalilin da ya sa yaran Borno da aka sace ba su samu irin kulawar jama’a da ta kafofin watsa labarai kamar yadda aka yi wa yaran Oyo ba duk da cewa an sace su a rana guda.
“An sace waɗannan yara a rana guda, amma babu wanda yake magana kan waɗanda aka sace daga Mussa ko kuma harin da aka kai makarantar Lassa kwanan nan. Muna buƙatar bayani,” inji shi.
Mustapha ya kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai a yaƙi da ta’addanci, tare da buƙatar gwamnati ta samar wa dakarun tsaro kayan aikin da suke buƙata domin kawo ƙarshen matsalar Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas.
