Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Kotun Masana’antu ta ƙasa da ke zamanta a Abuja ta umarci Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya da ta tura aƙalla lauya guda ɗaya zuwa kowane ofishin ‘yan sanda a faɗin ƙasar nan, domin aiwatar da tanadin da ke cikin Dokar ‘Yan Sanda ta 2020.
Alƙali Mai Shari’a O. Y. Anuwe ne ya bayar da wannan umarni a ranar Juma’a yayin da yake yanke hukunci a ƙarar da Amintattun Wakilan ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA) suka shigar a gaban kotu, inda suka kai ƙara kan Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda da wasu ƙarin waɗanda ake ƙara.
Kotun ta kuma haramta wa jami’an ‘yan sanda da ba sa cikin Sashen Lauyoyi na Musamman na Rundunar ‘Yan Sanda (Specialist Legal Cadre) wakiltar rundunar a shari’o’in farar hula.
Haka kuma, kotun ta yi watsi da ƙorafin farko da Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda ta gabatar, inda ta yi ƙalubalantar sahihancin ƙarar da kuma ikon ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya na shigar da ita.
ƙarar, wadda Sashen Shari’o’in Muradun Jama’a da Ci Gaban Doka na ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA-SPIDEL) ya shigar, ta nemi kotu ta yi fassarar wasu tanade-tanade na Dokar ‘Yan Sanda ta 2020, Dokokin Da’a na Masu Aikin Lauya na 2023, da kuma Police Force Order na 2013, musamman waɗanda suka shafi naɗin lauyoyin ‘yan sanda da irin ayyukan da ya kamata su riƙa yi.
ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya ta bayyana cewa jami’an ‘yan sanda da dama da aka ɗauka aiki a matsayin jami’an gudanar da ayyuka na yau da kullum (General Duty Officers), daga baya sun zama ƙwararrun lauyoyi, amma ba a sauya su zuwa Sashen Lauyoyi na Musamman kamar yadda doka ta tanada ba, duk da cewa suna gudanar da ayyukan shari’a tare da wakiltar rundunar a kotuna.
A hukuncinsa, Mai Shari’a Anuwe ya ce ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya tana da cikakken ikon shigar da irin wannan ƙara ta muradun jama’a, domin manufarta ita ce kare mutuncin sana’ar lauya da kuma tabbatar da bin tanadin doka.
Kotun ta ƙara da cewa jami’an ‘yan sanda masu ilimin lauya da ba a naɗa su ko sauya matsayinsu zuwa Sashen Lauyoyi na Musamman ba, ba su da hurumin ci gaba da wakiltar rundunar a shari’o’in farar hula, tana mai cewa hakan ya saɓa wa Dokokin Da’a na Masu Aikin Lauya.
Har ila yau, Mai Shari’a Anuwe ya bayyana cewa tura lauyoyi zuwa dukkan ofisoshin ‘yan sanda zai ƙarfafa sa ido kan bin doka, kare haƙƙin ɗan Adam, da kuma inganta yadda ake gudanar da kama mutane, bincike da tsare-tsare a hannun ‘yan sanda.
Da take martani kan hukuncin, ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA) ta bayyana shi a matsayin babbar nasara ga tabbatar da mulkin doka da kuma gyaran tsarin aikin ‘yan sanda.
A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na ɗ a ranar Asabar, ƙungiyar ta ce hukuncin zai taimaka wajen ƙara ƙwarewa a aikin lauyoyin ‘yan sanda, da sauƙaƙa samun shawarwarin shari’a a ofisoshin ‘yan sanda, tare da ƙarfafa kare haƙƙoƙin da Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya ya tanada.
