Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da tsohon Shugaban ƙasa na mulkin soja, Janar Yakubu Gowon, tare da wasu manyan baki, sun bayyana cewa marigayi tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya kasance shugaba mai kishin ƙasa wanda ya fifita muradun Nijeriya sama da bukatun kansa ko na yankinsa.
Sun bayyana hakan ne a taron tunawa da cikar shekara guda da rasuwar Buhari tare da ƙaddamar da littafin “Tributes and Condolences in Honour of Former President Muhammadu Buhari” da aka gudanar a Cibiyar Nazarin Sojojin Nijeriya da ke Abuja.
A jawabin da Mataimakin Shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya gabatar a madadin Shugaba Tinubu, shugaban ya bayyana Buhari a matsayin mutum mai jajircewa, kishin ƙasa da gaskiya wanda ya yi wa Nijeriya hidima ba tare da tunanin abin da ƙasar za ta mayar masa ba.
Tinubu ya ce shi da Buhari sun kasance abokan tafiya a harkokin siyasa da ci gaban ƙasa, inda suka yi aiki tare domin ganin an gina Nijeriya mai ci gaba da haɗin kai.
Ya ce Buhari ya ba da duk abin da yake da shi domin hidimar ƙasa, tun daga lokacin da yake shugaban mulkin soja har zuwa lokacin da ya zama shugaban ƙasa a tsarin dimokuraɗiyya.
Shugaban ya ƙara da cewa ko bayan ya sauka daga mulki, Buhari ya ci gaba da samun ƙauna da amincewa daga talakawan Nijeriya, lamarin da ya nuna irin amana da mutuncin da ya gina a tsawon rayuwarsa.
Tinubu ya yi addu’ar Allah Ya gafarta masa tare da bai wa iyalansa haƙurin jure rashin da suka yi.
A nasa jawabin, tsohon Shugaban ƙasa Janar Yakubu Gowon ya ce Buhari ya yi iya ƙoƙarinsa wajen yi wa Nijeriya hidima, yana mai bayyana shi a matsayin shugaba mai gaskiya da adalci wanda ya kasance yana fifita muradun Nijeriya sama da bukatun kansa ko na yankinsa.
Gowon ya tuna cewa ya daɗe yana hulɗa da Buhari tun lokacin da suke aikin soja tare, inda ya bayyana shi a matsayin jajirtaccen soja kuma shugaba mai mutunci.
Ya kuma yabawa rawar da Shugaba Tinubu ya taka wajen taimakawa Buhari ya zama shugaban ƙasa, yana mai cewa Buhari ma ya mayar da wannan alheri ta hanyar mara wa Tinubu baya domin ya gaje shi a mulki.
A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Katsina, Dakta Dikko Umaru Radda, wanda Mataimakinsa Faruk Lawal Jobe ya wakilta, ya ce al’ummar Katsina na alfahari da rayuwar Buhari da irin kyawawan dabi’u da ya bari a baya.
Ya bayyana Buhari a matsayin shugaba mai gaskiya, ladabi, riƙon amana da kishin ƙasa wanda ya yi aiki tukuru wajen inganta harkokin ababen more rayuwa, noma, yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma tsaro.
Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma shugaban kwamitin shirya taron, Boss Mustapha, ya gode wa Shugaba Tinubu, tsofaffin shugabannin ƙasa da sauran manyan baƙi da suka halarci taron domin girmama marigayi Buhari.
Ya bayyana cewa iyalan Buhari na shirin kafa gidauniyar Muhammadu Buhari Foundation and Centre domin ci gaba da adana tarihinsa da gudummawar da ya bayar wajen gina Nijeriya.
A nata jawabin, ‘yar marigayin, Safina Muhammadu Buhari, ta ce iyalan Buhari za su ci gaba da kare da kuma yaɗa kyawawan dabi’un da mahaifinsu ya rayu da su, musamman gaskiya, riƙon amana, adalci da sadaukar da kai wajen yi wa al’umma hidima.
Ta kuma bayyana cewa an bayar da kuɗaɗen da aka samu daga sayar da littafin “From Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammadu Buhari” domin gina cibiyar nazarin kimiyyar kwamfuta a Jami’ar Al-ƙalam da ke Katsina.
Safina ta ce aikin zai ƙunshi babban ɗakin taro mai ɗaukar mutum 200, dakunan karatu biyu, dakunan gwaje-gwajen kwamfuta guda uku da sauran muhimman kayayyakin more ilimi.
Ta gode wa mahaifiyarsu, Hajiya Aisha Buhari, bisa yadda ta jagoranci iyali bayan rasuwar marigayin tare da cika wasu daga cikin burinsa na raya ilimi da ci gaban al’umma.
