
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta yi watsi da ƙarar da ke neman tilasta wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta amince tare da bayyana sunayen Kwamitin riƙo na Jam’iyyar PDP, wanda Kabiru Turaki ke jagoranta da tsaginsu ya shigar a gabanta.
Mai Shari’a Salim Ibrahim a yayin hukuncin, ya bayyana cewa masu shigar da ƙarar waɗanda Shugaban Kwamitin Amintattu na PDP, Sanata Adolphus Wabara, ke jagorantar su, ba su da hurumin shigar da ƙarar.
Akan haka ne kotun ta yi watsi da ita bisa rashin ikon sauraron ƙarar a dokance, lamarin da ya jefa yunƙurin tsayawa takarar shugaban ƙasa na tsohon Shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan.
Haka kuma, kotun ta amince da ƙorafin da INEC ta gabatar mata da fari tare da goyon bayan irin wannan ƙorafi daga wasu bangarorin da ke son shiga cikin shari’ar.
Ta yi hukuncin cewa masu shigar da ƙarar sun gaza tabbatar da cewa INEC ta amince da wannan kwamitin riƙon, ko kuma suna da ikon shigar da ƙarar a madadin jam’iyyar PDP a matakin ƙasa.
