Fadar Shugaban Ƙasa ta faɗi yadda rashin jituwar sojoji a malkin Buhari ya haifar wa yaƙar ta’addanci tasgaro

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mai taimaka wa Shugaban Ƙasa akan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Daniel Bwala ya yi zargin cewa hamayya tsakanin Rundunar Soji da Rundunar Sojin Sama na Nijeriya a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa, Marigayi Muhammadu Buhari ya yi sanadiyyar hana wa dakarun tsaro tallafin jiragen sama na yaƙi a lokutan wasu atisaye.

Bwala ya yi iƙirarin cewa rashin jituwa tsakanin ɓangarorin jagoranci biyun a lokacin ya taimaka wajen haddasa tsaiko da rashin samun amsa daga ɓangaren dakarun tsaro a duk lokacin da suka nemi agajin sama yayin wasu atisaye.

Mai taimaka wa shugaban ya bayyana haka ne a wata hira da ta gidan talabijin, inda ake tattaunawa muhimman batutuwan ƙasa tsakanin manyan jami’an gwamnati a ranar Juma’a.

A cewarsa, an samu saɓani tsakanin Shugaban Rundunar Sojin Sama da jagorancin Sojoji (NA), lamarin da ya sa ayyukan haɗin-gwiwa a fage fama ya samu rashin nasara, inda yanzu kuma an samu sauyi.

Bwala ya yi waɗannan kalamai ne a lokacin da yake amsa tambaya zargin cewa ko ƙungiyoyin ‘yan ta’adda sun fi ƙarfin sojoji ne.

Akan haka ne ya yi watsi da iƙirarin inda ya ce dakarun tsaro na lallasa ‘yan ta’adda, yana mai bayyana zarge-zargen a matsayin zato da babu hujja a kai.

By Babaji

Leave a Reply