Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Rahotanni daga kafafen watsa labarai daban-daban sun rawaito Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio yana danganta ƙaruwar taɓarɓarewar tsaro da ake fuskanta a kasa na da alaƙa da shiga kakar zaɓe da ake ciki, inda yake nuni da cewa abubuwan da ke faruwa an shirya ne domin daƙile ayyukan alherin da gwamnati mai ci ke yi. Yana mai cewa rikice-rikice na ƙaruwa ne saboda wasu ‘yan adawa na ɗaukar nauyin hakan, har yana hasashen cewa da zarar an kammala hidindimun Babban Zaɓen 2027 cikin makonni biyu za a ga komai ya dawo daidai.
Waɗannan kalamai na Shugaban Majalisar Dattawa sun tayar da ƙura sosai, kuma sun hassala mutane da dama inda wasu ke bayyana takaici game da yadda ya nuna rashin damuwa da haƙiƙanin halin rashin tsaro da ƙasar ke ciki, duk da matsayin da yake kai na mutum na uku a Nijeriya. Yayin da wasu ke ganin hakan a matsayin wata hanya ta siyasantar da matsalar tsaro, don ɓoye gazawar gwamnati wajen shawo kan matsalolin tsaro da ke cigaba da durƙusar da cigaban ƙasar nan.
Akpabio ba shi ne kaɗai yake da wannan tunani ba, da dama daga cikin ’yan siyasa na ganin duk abubuwan da ke faruwa siyasa ce da neman madafun iko suke haddasa su. Akwai wasu da ke tunanin wai matsalar ɓarayin daji ta samo asali ne daga ƙoƙarin da tsohon shugaban ƙasa marigayi Muhammadu Buhari na sai ya hau mulki ta kowanne hali, shi ya sa ya ƙirƙiro da ƙungiyar ’yan bindiga don ɓata wa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan mulki. Bayan Buhari ya hau mulki, a cewarsu sai ya kasa cika alƙawarin da ya yi musu, hakan ya sa su yin bore da amfani da makamin da ya ba su akan gwamnatin sa. Ko a wannan gwamnatin ma akwai masu tunanin tsanantar ayyukan ta’addanci a arewacin ƙasar nan, na da alaƙa da yadda ’yan Arewa ke adawa da mulkin Bola Tinubu, suna ganin idan ba su ba ne a mulki babu wanda zai zauna lafiya.
Haka za ka riƙa jin ire-iren waɗannan maganganun a Jihar Filato inda rikicin ƙabilanci da na addini suka hana jihar cigaba da samun zaman lafiya. Akwai masu hasashen cewa ai ana samun rikici ne, saboda Hausawa sun nace sai sun zama ’yan ƙasa a jihar. Ko kuma saboda suna son su ƙwace mulki a ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa ne, yayin da wani sabon salon ya ɓullo yanzu kan cewa, Musulmi a jihar naso ne lallai sai an basu Mataimakin Gwamna. Kun ga duk waɗannan bayanai ne dake da alaƙa da siyasa, kuma wani lokaci ana faɗarsu ne don kawar da tunanin mutane daga musabbabin damuwar, domin wasu tsiraru su samu zarafin cimma muradinsu.
Ba zai yiwu a raba rikice-rikicen da suke faruwa da siyasa ba a wani ɓangaren, amma ɗora laifin samuwar tushen matsalar da wasu abubuwa masu nasaba da hakan kacokam kan siyasa, wannan kuskure ne. Kuma yana ma iya zama yaudara da cin amanar ƙasa.
Lallai ne a yarda da cewa jami’an tsaro na samun nasarori akan ’yan ta’adda a ƙasar nan, musamman a yankunan Arewa Maso Gabashin ƙasar nan da yankin Arewa Maso Yammaci, sai dai duk da haka akwai abubuwan fargaba da tashin hankali da ke ƙara bayyana game da sha’anin tsaro, ba kamar yadda gwamnati ke so mu yi tunanin nasarorin da ake samu sun fi ƙalubalen da ake fuskanta ba. Ga duk me nazarin abubuwan da ke faruwa a ƙasar nan ya san akwai matsala sosai da ke barazana ga sha’anin tsaro a rayuwar ’yan Nijeriya, wanda ke buƙatar gwamnati da jami’an tsaro su ƙara ninka ƙoƙarin da suke yi.
Babu wanda zai yi musun cewa, ana samun nasara akan ’yan ta’adda, akwai cigaba sosai da ake samu saɓanin a watannin baya. Amma duk da haka ba zai hana a bai wa gwamnati shawara ba, kodayake babu abin da ba ta sani ba.
Lallai akwai buƙatar amfani da sabbin makamai da aka ƙera da sabuwar fasahar zamani, don kai samame da saurin kai ɗaukin gaggawa, da tattara muhimman bayanai, da za su taimaka a samu galaba kan marasa son zaman lafiya a ƙasar nan.
Muna fatan Gwamnatin Tarayya ba za ta maimaita kuskuren da tsohuwar gwamnatin Goodluck Jonathan ta yi ba, inda ta siyasantar da batun Boko Haram, tana kallonsa a matsayin wani makirci ne na ’yan Arewa don hana mulkinsa zaman lafiya. Wannan sakaci shi ya bayar da damar da ƙungiyar ta samu na yin ƙarfi da mamaye wurare da dama, da haifar da asarar ɗimbin rayuka da dukiyar da ba a san adadinta ba. Wannan tunani ya fara shigowa cikin wannan gwamnati mai ci, inda wasu da suke ganin magoya bayan shugaban ƙasa ne, suna faɗar irin waɗancan maganganu da a baya aka zargi ’yan Arewa da su.
Siyasantar da sha’anin tsaro ko alaƙanta shi da wani shiri na kawar da wata al’umma saboda dalilai na addini, babban kuskure ne da shugabanninmu ke yi. Tunanin su kawai shi ne siyasar su da neman goyon bayan jama’ar su, ba sauke nauyin da kundin tsarin mulkin ƙasa ya ɗora musu ba. Kuskure ne a samu wani ɗan siyasa da zai riƙa maganganu na tunzura mutanensa akan wani addini ko ƙabila, yana mai ɗora alhakin gazawar tsaro a kan wasu mutane, don ba addininsu ko ƙabilarsu ɗaya ba.
Maganin matsalar tsaron da ake fuskanta shi ne kowa ya sa hannu a taimakawa gwamnati da jami’an tsaro, don shawo kan waɗannan matsaloli, a maimakon nuna yatsa ga wani ɓangare na ’yan adawa ko wata ƙabila. Haƙƙin kowa ne ya ba da gudunmawa a kowanne mataki, da dukkan damar da muke ita.
Allah Ya ba mu zaman lafiya da tsaro mai ɗorewa a jihohinmu da ƙasar mu bakiɗaya.
