Taya murnar Kirsimeti da sabuwar shekarar 2026

Spread the love

Bukukuwan Kirsimeti da ma na shigowar sabuwar shekara lokaci ne mai matuƙar muhimmanci ga al’ummar Kiristoci a sassan duniya, lokaci da ke ɗauke da zurfin ma’ana ta godiya, nuna ƙauna da soyayya. Wannan lokaci na musamman na tunatar da Kiristoci haihuwar Annabi Isa Almasihu, wanda rayuwarsa da saƙonsa suka ginu ne a kan ƙauna, yafiya, tausayi da kuma zaman lafiya tsakanin mutane. Kirsimeti ba biki ne na shagali kawai ba, illa wani muhimmin lokaci ne na nazari da waiwayen ɗabi’u da ya kamata su zama tubalin rayuwar al’umma.
A haƙiƙanin gaskiya, Kirsimeti ba na Kiristoci kaɗai ba ne. Lokaci ne da ke ba da damar dukkan al’umma, ba tare da la’akari da bambancin addini, ƙabila ko ra’ayi ba, su tsaya su yi tunani kan muhimmancin zaman tare cikin fahimta da mutunta juna. A ƙasa irin Nijeriya, wadda ke ɗauke da bambancin addinai, al’adu da harsuna, irin wannan lokaci na da matuƙar tasiri. Kirsimeti na tunatar da mu cewa bambancin da ke tsakaninmu bai kamata ya zama dalilin rarrabuwa ko rikici ba, sai dai wata hanya ta ƙarfafa haɗin kai da gina ƙasa dunƙulalliya.
Saƙon Kirsimeti na ƙauna da zaman lafiya ya zo ne a lokacin da duniya gaba ɗaya ke fuskantar ƙalubale masu tarin yawa. A Nijeriya, ana fama da matsaloli na tattalin arziki, tsaro, tsadar rayuwa da kuma rashin jituwa a wasu sassa. A irin wannan yanayi, darussan da Kirsimeti ke koyarwa sun fi dacewa fiye da kowane lokaci. Saƙon jinƙai ga mabuƙata, taimakon marasa galihu da kula da juna ba tare da tambayar addini ko ƙabila ba, ɗabi’u ce da ka iya rage raɗaɗin ƙalubalen da al’umma ke ciki.
A yayin da Kiristoci ke gudanar da bukukuwan Kirsimeti, ana sa ran wannan lokaci ya zama dama ta sake gina alaƙa tsakanin mutane. Yana da muhimmanci iyalai su ƙara kusantar juna, al’umma su ƙara fahimtar juna, tare da mayar da hankali kan abubuwan da ke haɗa mu, ba waɗanda ke raba mu ba. Kirsimeti na koyar da cewa soyayya ba ta da iyaka, kuma zaman lafiya ba ya tabbata sai an yi haƙuri, an yafe, an kuma mutunta juna.
Shigowar Sabuwar Shekara kuma na zuwa ne ɗauke da sabon fata da sabbin buri. Lokaci ne da ya dace kowa ya waiwayi shekarar da ta gabata, ya duba inda aka yi kuskure da inda aka samu nasara, domin ɗaukar darasi zuwa gaba. Sabuwar Shekara na nuni da sabon farawa, sabon tunani da kuma ƙudurin gyara kai da al’umma baki ɗaya. Ga ƙasa irin Nijeriya, Sabuwar Shekara na buƙatar ƙarin haɗin kai tsakanin ‘yan ƙasa domin fuskantar ƙalubale tare da gina makoma mai ɗorewa.
Sabuwar Shekara ba wai sauyin kwanan wata kawai ba ce, sauyin tunani da ɗabi’a ce. Lokaci ne da ya kamata a ƙara jajircewa wajen gina ƙasa bisa gaskiya, adalci da riƙon amana. Idan kowane ɗan ƙasa ya ɗauki alhakin yin abin da ya dace a matsayinsa, ko a gida, ko a wurin aiki, ko a cikin al’umma, to babu shakka za a samu canji mai kyau. Wannan shi ne ainihin ruhin Sabuwar Shekara da ya kamata ya wuce maganganu zuwa aikace-aikace.
A matsayinta na ƙasa ɗaya, Nujeriya na buƙatar zaman lafiya fiye da komai. Addini, ko da kuwa ya bambanta, ya kamata ya zama ginshiƙin gyara rayuwa da haɗa zukata, ba hanyar rarrabuwa ba. Kirsimeti na tunatar da mu cewa addini, Musulunci ko Kiristanci na koyar da ƙauna da tausayi, ba ƙiyayya da rikici ba. Idan aka rungumi wannan darasi, za a gina al’umma mai fahimtar juna da zaman lafiya mai ɗorewa.
Hakazalika, akwai buƙatar shugabanni da masu faza a ji su yi amfani da irin wannan lokaci wajen ƙarfafa saƙon haɗin kai da zaman lafiya. Maganganu da ayyuka masu nuna adalci, mutunta juna da gaskiya za su taimaka wajen gina amincewa tsakanin al’umma tare da rage fargaba da rashin jituwa. Kirsimeti da Sabuwar Shekara su zama dama ta sabunta alƙawarin gina ƙasa bisa hidima, gaskiya da ƙishin jama’a.
A ƙarshe, muna taya ɗaukacin Kiristoci murnar bikin Kirsimeti tare da yi musu fatan shigowar Sabuwar Shekara cikin ƙoshin lafiya, nasara da albarka. Muna kuma fatan wannan lokaci zai ƙara danƙon zumunci tsakanin ‘yan Nijeriya, tare da samar da ƙarin fahimta, haƙuri da haɗin kai. Allah Ya sa shekarar da ke tafe ta zama shekarar zaman lafiya, ci gaba da dunƙulewar ƙasa, inda kowa zai samu damar rayuwa cikin mutunci da kwanciyar hankali.
Allah Ya ba mu ikon zama jakadun zaman lafiya a duk inda muke.

By ukarofi