Gwamna Yusuf ya taya Kiristocin Kano murnar Kirsimeti

Spread the love


Daga RABIU SANUSI a Kano
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya taya al’ummar Kirista da ke Jihar Kano da ma faɗin Nijeriya murnar bikin Kirsimeti na shekarar 2025 inda ya bayyana lokacin a matsayin na soyayya, sadaukarwa, haɗin kai da zaman lafiya a tsakanin al’umma.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanya wa hannu a ranar Alhamis.
Gwamna Yusuf ya ce bikin Kirsimeti na ba da muhimmiyar dama ta tunani kan muhimman ƙimomin zaman lafiya, haƙuri, tausayi da hidima ba tare da son rai ba, waɗanda ya jaddada cewa su ne ginshiƙan zaman tare cikin jituwa a al’umma mai cike da bambance-bambancen addini da ƙabila kamar Jihar Kano.
Ya buƙaci al’ummar Kirista a jihar da su yi amfani da wannan lokaci na bukukuwa wajen ƙara yaɗa saƙon zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban bai ɗaya tare da yin kira ga dukkan mazauna jihar, ba tare da la’akari da bambancin addini ko ƙabila ba da su ci gaba da rayuwa cikin mutunta juna da fahimtar juna.
Gwamnan ya kuma tabbatar da aniyar gwamnatinsa na kare haƙƙin kowane ɗan ƙasa tare da samar da yanayi mai inganci da kowa zai samu ’yancin gudanar da addininsa cikin kwanciyar hankali.
Haka kuma Gwamna Yusuf ya yi kira ga shugabannin addinai da su ci gaba da wa’azin haƙuri da zaman lafiya yana mai jaddada cewa haɗin kai shi ne ginshiƙi mafi ƙarfi wajen samar da ci gaba mai ɗorewa a Jihar Kano.
Ya yi wa al’ummar Kirista fatan murnar Kirsimeti cikin farin ciki tare da yin addu’ar samun sabuwar shekara mai albarka, zaman lafiya da bunƙasa ga dukkan al’ummar jihar.
A ƙarshe, gwamnan ya shawarci direbobi da su kiyaye dokokin zirga-zirgar ababen hawa a tsawon lokacin bukukuwa da bayan su domin tabbatar da tsaro da kare rayuka a kan tituna.

By ukarofi