Shekaru goma sha biyu bayan mummunan harin da ya girgiza duniya a garin Chibok da ke Jihar Borno, al’amarin sace ɗalibai a Nijeriya ya ci gaba da zama babban ƙalubale ga tsaro da ilimi, tare da barin tambayoyi masu nauyi kan yadda za a dawo da amincewar jama’a ga tsarin kariya da gwamnati ke da shi.
A daren 14 ga Afrilu, 2014, mayaƙan ƙungiyar Boko Haram sun kai hari makarantar sakandiren mata ta gwamnati da ke Chibok, inda suka yi awon gaba da ɗalibai 276 masu shekaru tsakanin 16 zuwa 18. Duk da cewa wasu 57 sun samu tserewa nan take, yawancinsu an kai su cikin dazukan Sambisa, abin da ya haifar da gagarumin zargi da tir da gwamnatin wancan lokaci.
Lamarin ya haifar da gangamin duniya na #BringBackOurGirls, wanda ya samu goyon bayan fitattun mutane da ƙungiyoyi na ƙasa da ƙasa, yana matsa lamba ga gwamnatin Nijeriya ta ɗauki matakin gaggawa. Sai dai martanin farko da aka bayar ya fuskanci suka mai tsanani, lamarin da ya ƙara raunana amincewar jama’a ga shugabanci.
Ko da yake an saki wasu daga cikin ’yan matan a matakai daban-daban daga 2016 zuwa 2024, har yanzu kimanin 100 daga cikinsu ba a san inda suke ba. Wasu rahotanni na nuna cewa wasu daga cikinsu sun mutu, yayin da waɗanda suka dawo suka bayyana irin azabar da suka sha, ciki har da tilasta musu aure, sauya addini da kuma cin zarafi.
Bayan faruwar lamarin Chibok, Gwamnatin Tarayya ta ɓullo da shirin Tsaron Makarantu (Safe Schools Initiative) domin kare makarantu daga hare-hare. Amma fiye da shekaru goma bayan haka, har yanzu makarantu a arewacin Nijeriya na fuskantar barazana, abin da ke nuna cewa shirin bai kai ga cimma burinsa ba yadda ake fata.
Tun daga lokacin, hare-haren sace ɗalibai sun yawaita a sassa daban-daban na ƙasar nan. Daga Dapchi a Jihar Yobe, zuwa Kankara a Katsina, Kagara da Tegina a Jihar Neja, har zuwa Jangebe a Zamfara da kuma Kuriga a Kaduna, ɗaruruwan ɗalibai sun faɗa hannun ’yan bindiga. Wasu an sake su, wasu kuma har yanzu suna hannun masu garkuwa da mutane, yayin da aka kashe wasu.
Rahotanni sun nuna cewa sama da ɗalibai 2,000 aka sace tun bayan lamarin Chibok, yayin da matsalar ta wuce makarantu zuwa ƙauyuka, hanyoyi da wuraren ibada, alamar yadda tsarin tsaro ya ƙara taɓarɓarewa.
Masana tsaro sun bayyana cewa gazawar gaggauta ɗaukar mataki a Chibok ta ƙarfafa gwiwar ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane, inda suka mayar da sace ɗalibai wata sana’a mai riba. Har ila yau, wasu rahotanni sun nuna cewa wasu hare-hare na iya zama an kauce musu idan aka ɗauki matakan da suka dace tun da wuri.
Tasirin wannan matsala ya wuce waɗanda abin ya shafa kai tsaye. Tsoron hare-hare ya sa iyaye da dama ke cire ’ya’yansu daga makaranta, musamman ’yan mata, abin da ya ƙara yawan yara marasa zuwa makaranta daga kusan miliyan 10 zuwa kusan miliyan 20 a cikin shekaru goma.
Wannan al’amari na nuna babbar barazana ga makomar ƙasar, domin rashin ilimi na iya haifar da talauci, rashin zaman lafiya da kuma ƙaruwar matsalolin tsaro a nan gaba.
A yau, abin da ake buƙata ya wuce tuna tarihi ko nuna tausayi. Nijeriya na buƙatar ɗaukar matakan gaggawa da masu auna sakamako domin kare makarantu, da ƙarfafa tsaro, da kuma inganta tsarin gano barazana tun da wuri. Haka kuma, dole ne a sake duba shirin Tsaron Makarantu cikin gaskiya da tabbatar da ana aiwatar da shi yadda ya kamata.
Fiye da komai, akwai buƙatar sake ƙarfafa ƙoƙarin kuɓutar da sauran waɗanda ke hannun masu garkuwa da mutane, ciki har da ’yan matan Chibok da har yanzu ba su dawo ba.
Har sai an cimma hakan, lamarin Chibok ba zai kasance tarihi kawai ba, sai dai wata alama ta gazawar da ke ci gaba da wanzuwa — alamar ƙasa da ta kasa kare ’ya’yanta.
