Talauci da rashin tarbiyya ke sa ake cin zarafin mata – CITAD

Spread the love

Daga ABBA MUHAMMAD a Kaduna

Cibiyar Fasahar Sadarwa da Cigaban Al’umma (Center For Information Technology and Development CITAD), ta shirya a Kaduna domin wayar da kan al’umma a kan cin zarafin mata da ƙananan yara, amma sun fi maida hankali a kan mata.

An gudanar da taron a ɗakin taro da ke cikin ginin gidan Marigayi Sir. Ahmadu Bello Sardauna, a Cikin Arewa House, Kaduna.

A yayin da ya ke zantawa da manema labarai ana tsaka da taron, ɗaya daga cikin ma’aikatan cibiyar, Malam Kamal Garba Alhassan ya bayyana cewa, “Talauci, rashin wayar da kan al’umma da rashin tarbiyya su ne manyan abubuwan da suke sa ake cin zarafin mata a zamanin nan.”

Kamal ya cigaba da cewa, “Duk wanda zai ci zarafin mace, in dai ya na da tarbiyya da mutunci, karanci da yakana ba zai yi ba, domin idan mutum zai yi, zai rinƙa kwatanta wa da kan sa cewa idan ‘ya ta ce ko Yahaya ce, ko ƙanwata ce ko ‘yar’uwata ce in aka yi min yaya zan ji? Ka ga ko da akwai talauci da sauran su, in akwai tarbiyya ba zai yi wannan abu ba. Sannan kuma yadda ake cewa wasu ayyuka na tsafe-tsafe suke sakawa ake yin wannan abu domin su kai ga cimma burin da suke nema a duniya.”

Ko ta wace hanya yake ganin za a magance waɗannan abubui?, sai ya ce, “Kamar yadda mu ke yawan faɗa ina muka je irin waɗannan taruka, iyaye su saka ido, su tabbatar sun yi wa ‘ya’yan su tarbiyya ta gari, su tabbatar su na zuwa makaranta, su tabbatar su na samun ilimi na gari.

Sannan kuma, abuƙarfi, ki yaushe ina aka tashi magana, sai an yi maganar gwamnati. Domin idan baka da gwamnatin da za ta tsaya ta tabbatar da cewa dalilin da yasa ake yin hukunci, ba wai don wanda ya yi laifi ake yin hukunci ba, saboda gobe kada wani ya yi wannan abin, shi ne dalilin da yasa ake yin hukunci. Wannan hukuncin da ake yi, in dai akwai dokoki, ba wai kawai dokoki da ake da su ba, yaya ake ɗabbaƙar da waɗannan dokoki, in ka san cewa in ka yi abu kaza za a yi maka kaza, in akwai mutum ɗari da ke so su yi wannan abin, casa’in da wani abu daga ciki za su ce ba za su yi ba. Ka ga an samu raguwar wannan abu. Ya zama mu na da dokoki masu kyau, iyaye su yi wa ‘ya’yan su tarbiyya, waɗannan su za su kawo sauƙin raguwar waɗannan abubuwa na cin zarafin mata.”

Shin ya ƙungiyar su ta ke tunkarar masu madafun iko da aka kama su da cin zarafin mata? Sai amsa da cewa, “Shi ne rashin aikin dokar kamar yadda na faɗa. In doka na aiki, ba ruwan ta Sarki, gwamna, Shugaban ƙasa da waye, doka ce za ta yi aiki. Shugabanci na gari ya fi komai, idan ka na da shugabanci na gari, shi shugaba ya san cewa idan ka yi laifi doka ta hau kan ka, an sha samun wasu in suka yi laifi sai su je su ɓuya a bayan wani, amma waɗannan ba su ba da dama sai su ce a’a, doka ce za ta yi ai. To idan ka na da shugabanci na gari mai kyau, ba za ka samu wannan abin ba, babu wanda zai ji daɗi, duk wani mai mutunci, karanci da sanin ya kamata ki da ɗan sa ne ya yi abu ba zai yarda da cewa doka ta ƙi aiki ba, domin shi ma za a yi akasin haka a kan ɗan’uwan da ko wani, ka ga idan ta faru doka bata aiki shi ma ba zai ji daɗi ba. Saboda haka ina dai shugabanni suka samu doka mai kyau, al-umma za su ji daɗi.”

Taron ya samu halartar Malaman addinin musulunci da na kirista. Haka kuma ya samu halartar ƙungiyoyin mata da kuma ƙungiyoyin kare hakkin mata da ƙananan yara.

Yayin gudanar da taron, an tattauna muhimman batutuwa da suka shafi cin zarafin mata, musamman ɓangaren fyaɗe. An ɗauki tsawon lokaci ana ɗauki ba daɗi wajen ganin yaya za a yi a magance wannan babban matsala da ta addabi al-umma.

Shugabannin ƙungiyoyi da kuma wasu manyan mata iyaye sun ba da shawarwari masu ma’ana da kuma yadda za a daina ɓoye lamarin idan ya auku. Inda wasu suka maida hankali a kan cewa duk wa da aka kama shi da laifin fyaɗe a tilasta shi ya auri yarinyar da ya yi wa fyaɗen, wasu kuma su na ganin cewa haka ba zai yiwu ba. Wasu kuma su na ganinta rufe maganar domin kada saka yarinyar cikin tashin hankali da damuwan al-umma.

Malam addini su ma sun ba da nasu gudunmawar ta yadda za a magance lamuran cikin sauƙi.

Taron ya ƙayatar, an kuma samu ilimi a ciki da kuma mafita a kan abubuwan da suka shafi cin zarafin mata.

Mahalarta taron sun yi wa ƙungiyar CITAD godiya da irin wannan gagarumin gudunmawa da suke ba al-umma na wayar da kai da kawo mafita ga al-umma.

An tashi taron da misalin ƙarfe 1:30 na rana.

By ukarofi