Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kebbi Alhaji Yakubu Ahmed Birnin Kebbi ya saka wuta mai aiki da hasken rana tare da yin feshin maganin sauro a Anguwar Rafin Atiku da cikin garin Birnin Kebbi.
Da ya ke zantawa da waƙilin jaridar Blueprint Manhaja, Hakimin anguwar Alhaji Hamza Ahmed BK ya yaba wa kwamishinan bisa ga wannan ƙoƙarin na nuna kulawa da al’umma.
Ya ce wannan hasken zai taimaka wajen hana ɓatagari yawo cikin anguwar saboda ba wajen laɓewa su yi ɓarna.
A ɗaya ɓangaren kuma wannan anguwar tana fama da matsalar sauro rani da damina saboda kwatocin da ke ajiye ruwa, wannan feshin zai kashe sauro da sauran ƙwari da ke kawo cutuka daban-daban.
Ya yi kira ga al’ummar anguwar da su saka ido kan waɗannan kayan da aka kafa kada su bari a lalata su. Ya yi kira ga sauran ƴan siyasa da su yi koyi da wannan kwamishinan na yaɗa labarai wajen kawo duk wani abu da zai amfani al’umma.
Alhaji Ahmed Yakubu Birnin Kebbi ya bayyana cewa yana da kyau ga duk wanda ya sami wata dama ya yi amfani da ita wajen kawo cigaba a cikin al’umma ta yadda zai bar tarihin da za rinƙa tunawa da shi.
Ya bayyana cewa wannan ya yi daidai da ra’ayin gwamna Malam Nasir Idris na aiwatar da ayukan cigaba ga al’umma.
