Burna Boy da Shakira za su yi waƙa yayin hutun rabin lokaci a wasan ƙarshe na Kofin Duniya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sanannen mawaƙin al’adun Afirka kuma ɗan Nijeriya, Burna Boy tare da shahararriyar mawaƙiyar nan ta ƙasar Kolombiya, Shakira, sun sake haɗuwa gabanin wasan ƙarshe na gasar Kofin Duniya na 2026, inda za su nishaɗantar da masu kallo yayin da aka tafi hutun rabin lokaci a wasan.

A wani bidiyo da Burna Boy ya wallafa a kafar X, an ga yadda mawaƙan duniyar biyu suke gaisawa cikin nishaɗi yayin da suke shirya wa gabatar da wasa a wasan ƙarshe na Kofin Duniyar.

Mawaƙin, wanda ya taɓa lashe kyautar Grammy, ya bayyana farin cikinsa akan gabatar da wasa tare da Shakira a ɗaya daga cikin manyan tarukan wasannin duniya.

Tuni dai Hukumar FIFA ta tabbatar da cewa ɗan Nijeriyar da Shakira za su jagoranci nishaɗantar da masu kallo da taken gasar.

Haka kuma, akwai wasu taurarin waƙa a matakin duniya waɗanda su ma za su shiga cikin gabatar da wasan ciki har da BTS, Madonna, Justin Bieber, Gustavo Dudamel, Coldplay’s PS22 Chorus, da kuma jaruman finafinan Sesame Street da The Muppets.

Akan haka ne ake sa ran hutun rabin lokacin wasan ƙarshen ya zama mai tsawon sama da mintina 15 da aka saba gani domin ba wa mawaƙan damar gudanar da harkokinsu cikin tsanake.

Wasan, wanda za a buga tsakanin Argentina da Sifaniya zai tara miliyoyin magoya baya daga sassan duniya yayin kallo, lamarin da zai bayar da damar kallon wasan mawaƙan.

By Babaji

Leave a Reply