Wata mata ta rasu bayan ta haifi ‘yan uku a Kebbi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Wata mata da ba a bayyana sunan ta ba daga ƙauyen Ƴangar Hausawa a mazabar Etene a ƙaramar hukumar Kalgo da ke jihar Kebbi ta rasu bayan ta haifi ƴan uku.
Malama Sarautu Labaran wata ‘yar uwar marigayiyar ta bayyana cewa jinjiran duka uku suna cikin ƙoshin lafiya sai dai kasancewar mahaifin su maras ƙarfi ne ba zai iya ɗaukar nauyin su ba.
Yanzu haka yaran suna babbar asibitin jiha da ke garin Kalgo ( KMC) domin samun kulawa da lafiyarsu .

Ta ce ‘yan uwan wannan matar suna neman taimako wajen gwamnati da kuma ƙungiyoyin sa kai domin cigaba da kulawa da waɗannan jinjiran guda uku domin samun kuzari da kuma ƙoshin lafiya.

By ukarofi

Leave a Reply