Daga UNCLE LARABI
Zuwa ga masu nema wa mijin Fatima, wacce aka kashe tare da ’ya’yanta shida a birnin Kano taimako; wato Barista Abba Hikima, Fauziyya D. Sulaiman, Rahma Abdulmajid da Umma Sulaiman AuntyBaby, ana ta maganar Malam Baba Haruna ana tara masa himilin kuɗi, kada a manta da iyayen matarsa, Fatima.
Idan Mahaifiyarta da mahaifinta suna raye, su ma suna cikin sahun farko da ba za su taɓa manta wannan mugun iftila’in ba. Ba za su iya barci mai kyau ba. Ba za su iya cin abinci, don yunwa ba. Kai hatta ’yan uwanta na jini da suke uwa ɗaya uba ɗaya wannan tabon zai fi shekara guda bai goge a cikin zuciyarsu ba.
Shawara; idan an duba Malam Baba Haruna Bashir, to a duba iyayen Fatima da suka tafka mummunar asara, idan har suna nan a raye. Tabbas mahaifiyarta ma za ta fi shi ji, tunda ita ba za a sake yi mata wata Fatima ɗin ba. Amma shi ga shi ana cewa a aura masa wasu matan. Ita kuma ba za a haifa mata wata Fatimar ba. ’Yan jarida su lalubo mahaifiyarta da mahaifinta, domin suna cikin damuwa su ma.
Uncle Larabi (Abdullahi Jibril Larabi) marubuci ne a Kano
