
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatinsa ba za ta taɓa lamuntar rashin ladabi ko cin mutunci ga jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ba a kowane yanayi.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wajen rabon tallafin babura ga matasa ’yan gwagwarmaya a jihar, inda ya ce Kwankwaso mutum ne da ya sadaukar da rayuwarsa wajen fafutukar adalci, ci-gaba da walwalar talakawa.
A cewarsa, girmama jagoranci da mutunta waɗanda suka kafa tubalin tafiya abu ne mai muhimmanci a siyasa.
Ya kuma yi gargaɗin cewa duk wani yunƙuri na raini ko cin mutunci ga Kwankwaso ba za a lamunce shi ba domin babu wajibi a tsare mutuncin masu mutunci.
Gwamnan ya kuma yi kira ga magoya baya da matasa da su cigaba da nuna ladabi, haƙuri da fahimtar juna, tare da kare martabar tafiyar da suka yi imani da ita.
Ya kuma ƙalubalanci gidajen jarida da su ƙaurace wa bada dama ga masu irin wannan ɗabi’ar ta cin fuska ga masu alfarma, yana mai cewa wajibi a kare martabar gwamnatinsa wajen kiyaye mutunci jagororin al’umma, kamar yadda Kakakinsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana a wata hira da manema labarai.
