Daga MOHAMMED BALA GARBA
Ban ce soyayya ƙarya ba ce, amma dai soyayyar da take gudana a yanzu tsakanin samari da ‘yan mata kusan duk bula (ƙarya) ce. Duk da ana samu ƙalilan da suke gudanar da na gaskiyar, amma ba su da yawa, mafi yawan su ta ƙarya suke gudanarwa. Dalilin da ya sa na ce haka shi ne, saboda babu komai a cikin soyayyar illa kalaman ƙarya da yaudara da rainawa juna hankali. Misali:
~ Duk duniya babu macen da ta kai ki a zuciyata.
~Kai ne dalilin da ya sa nake murmushi a kowanne lokaci.
~Kallo ɗaya daga gare ki yana iya sa zuciyata ta buga da sauri.
~Idan babu kai a rayuwata, kamar babu numfashi ne.
~Babu abin da yake faranta min rai kamar murmushinki.
~Idan aka haɗa jin daɗin duniya gabaɗaya, ba zai kai jin daɗin kasancewa tare da kai ba.
~Zuciyata na buguwa ne da tunaninki a kowanne lokaci.
~Kai ne ruhina, kai ne numfashina.
~ Don ke Allah ya halicci ni, da dai sauran ire-iren waɗannan kalaman na ƙaryayyaki (waɗanda kun fi ni saninsu) da ake gina tubalin soyayyar da su, wanda kuma su ne mu’assasin yawan samun matsalolin da ake samu a gidan auren yau.
Ka ce mata duk duniya babu macen da ta kai ta a zuciyarka; alhalin kasan ƙarya kake. Mahaifiyarka ta fi ta. Ita ma ta ce maka kai ne dalilin da ya sa take numfashi, bayan ta san ƙarya take. Domin ko mutuwa ka yi, za ta cigaba da numfashi. To don haka mene ne amfanin yi wa juna ƙarya?
Na taɓa tambayar wata abokiyar karatuna a jami’a, na ce mata, tsakanin soyayya da kulawa wanne kike buƙata a wajen mijinki?
Sai ta ce, “Kamar ya ya! Akwai bambanci ne tsakanin soyyaya da kulawa?”
Na ce mata, ƙwarai akwai. Soyyaya shauƙi ce ta zuciya wacce tana gushewa; yayin da kulawa kuma wani abu ne da yake samuwa daga aminta ko kuma amincewa. Akwai macen da za ka iya son ta, ko don diri/kyau, kuɗi, tarbiyya, asali ko kuma ilimi, amma kuma ba za ka taɓa yarda ka rayuwa da ita a matsayin mata ba. Akwai kuma wacce za ka iya son ta, don waɗannan abubuwan, tare kuma da burin ku rayu da ita a matsayin ma’aurata. Wannan shi ne soyayya, daga shauƙi yake samuwa. Amma yana gushewa.
Shi kuwa kulawa, daga aminta/amincewa yake samuwa. Da farko sai ka amince da mutum, sannan za ka iya ba sa wani abinka ya kula maka da shi. Kafin ka amince da mutum, akwai abubuwan da ake dubawa kamar su: ƙwarewa, ilimi, alƙawari, hankali, da kuma amana da yarda, sannan ka ɗauki abin ka ba sa ya kula maka shi. Saɓanin soyyaya, da za ta iya ingiza mace ta auri marar ilimi, hankali, alƙawari, tarbiyya, nutsuwa da kuma amana. Ana faɗa mata illar auren shi, tana cewa ‘ta ji ta gani tana so. Dukan matansa yake, ta ce ni ba zai dake ni ba. Daga ƙarshe kuma idan ta shiga gidansa, ya casata. Soyyaya kenan.
Shi kuwa kulawa, yana sa mace ta aure ka matuƙar ta aminta da kai ko babu soyayya. Iyayenmu na can baya, da kakaninmu, irin wannan auren aka musu. Babu soyayya, sai dai aminta, kuma suka samu kulawar da sai dai na yanzu su ji labari. Akwai mata da dama a wancan lokacin, da sai da mazajensu suka shigo ɗakunansu a daren farko sannan suka san su ne mazajensu, saboda aminta. Amma a haka, suka rayu sama da shekaru saba’in ba tare da ta taɓa yin yaji ba. Saɓanin yanzu, ‘yan bani-na-iya, ‘ya’yan zamani, masana soyayya, masu tutiyar wayewa da ilimin boko. Sai a shekara biyar ana tafka uban soyayya, har ma a haɗa da uwar a kusa tsokano kakar, amma da zarar an yi aure, ka ga a kasa zaman shekara guda lamin lafiya.
Don haka, ki tambayi kanki, kulawa ya kamata ki samu a wajen mijinki ko kuma dai soyyaya?
Ni dai na yi gaba.
Mohammed Bala Garba manazarci kuma marubuci ne daga Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno,
14 ga Junairu, 2026
