
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Juma’a Mazauna yankunan Woro da Kaiama a Jihar Kwara suka yi cincirindo domin tarbar mutanen Woro 146 da aka yi garkuwa da su, inda suka shiga rawa, kiɗa da murna yayin sake haɗuwa da su. Jama’a da dama sun yi maraba lale da ganin ‘yan uwa da abokansu tare da zubar da ƙwallar farin ciki.
Rahotanni sun bayyana cewa, gwamnatin Jihar Kwara ta ba wa waɗanda abin da ya shafa tallafin Naira miliyan 80 bayan kwana 21 ana duba lafiyarsu. An ba wa kowane ɗaya daga cikinsu N200,000 zuwa miliyan N1, inda manya za su samu miliyan N1 kowanne, matasa N500,000 sai kuma yara N200,000 domin ba su damar sake gina rayuwarsu.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Kaiama, wanda kuma shi ne Shugaban Ƙungiyar Ƙananan Hukumomi ta Ƙasa (ALGON), reshen Jihar Kwara, Alhaji Abdullahi Danladi ne ya bayyana hakan a fadar Sarkin Kaiama yayin murnar komawar mutanen cikin ‘yan uwansu.
Ya kuma yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq bisa ƙoƙarinsu wajen tabbatar da an ceto mutanen bisa aminci da kuma kula da lafiyarsu.
Ya bayyana cewa, baya ga 146 da suka koma gidajen nasu, akwai guda uku kuma da suke asibiti suna karɓar magani, yana mai kira ga jama’a da su tallafa wa mutanen tare da ƙarfafa musu gwiwa domin farfaɗowa daga halin da suka samu kansu a ciki kafin wannan lokaci.
