Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ɗimbin tubabbun ‘yan bindiga suka halarci bikin naɗin Sabon Sarkin Ruma, Hakimin Batsari Alhaji Sani Tukur a Jihar Katsina.
Bikin da ya gudana a fadar Sarkin Ruma a garin Batsari ya biyo bayan naɗin sa da wasu sabbin hakimai shida mai martaba Sarkin katsina ya yi a fadar sa.
Al’ummar yankin Batsari na ganin fitowar tubabbun ‘yan bindigan su halarci bukukkuwan a garin Batsari ya jawo hankulan al’umma da sarakunan yankin.
Shagulgulan bikin sun haɗa da hawan dawakai da wasu wasannin gargajiya ya gudana a fadar Sarkin Ruma a inda tubabbun ‘yan bindigan suka kai gaisuwar ban girma da jaddada goyon baya ga sabon hakimin da tabbatar da dauwamamman zaman lafiya a yankin.
Ɗaya daga cikin tubabbun ‘yan bindiga Tukur ya bayana jin daɗin sa kan haɗin kai da zaman lafiya da yake wanzuwa a tsakanin su da al’ummar gari.
Ya bayyana Batsari a matsayin babban gari mai ɗimbin tarihi, sai ya taya Sarkin Ruma murna da wannan naɗin.
Gawurtaccen ɗan bindiga a yankin Bala Musa eanda shima ya halarci bikin ya nuna cigaba da aka samu wajen maido da zaman lafiya a yankin.
