An halaka ‘yan ta’adda 26, sojoji huɗu sun jikkata yayin da dakaru suka daƙile hari a Borno

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Dakarun tsaro na Atisayen Haɗin Kai a Arewa maso Gabas, sun yi nasarar halaka ‘yan ta’adda guda 26 yayin daƙile wani hari a Jihar Borno, kamar yadda masanin harkar tsaro, Zagazola Makama ya bayyana a wani rahoto.

Al’amarin ya faru ne a yankin ƙauyen Kadiya da ke Ƙaramar Hukumar Kukawa a daren Juma’a wayewar Asabar. A cewar rahoton, ‘yan ta’addan sun yi arangama ne da dakarun tsaron Bataliya ta 101 sojoji na musamman da misalin ƙarfe 10:45 na daren yayin yunƙurin kai wa yankin farmaki.

Wasu majiyoyin soji sun shaida wa Makama cewa sojojin sun yi nasarar ne yayin da suka mayar da martani da sama da ƙasa, matakin da ya tilasta wa maharan janyewa daga kai farmakin nasu. A yayin haka ne sojojin sama suka yi luguden wuta akan ‘yan ta’addan, waɗanda suke tserewa ta yankin Tunbuns/Kangarwa da wasu da suka fake a ƙarƙashin bishiyoyi.

Farmakin sama biyu sun yi ajalin ‘yan ta’adda 25 da lalata babura 10 da suka yi jigilar su. A lokacin da dakarun tsaron suke biko a washe-garin ranar da safiyar Asabar, sun ci karo da gawar wani ta’adda, wanda hakan ya kai jimillar waɗanda aka halaka zuwa 26.

Haka kuma, sojojin sun ƙwato wasu muggan makamai da wasu ababe yayin atisayen ciki har da alburusan 7.62 x 54mm guda 253, alburusan 7.62mm guda 12 da wasu guda biyu na harin jirgin sama. Sauran ababen da aka ƙwato sune jakar baya, makarin ido, tabarau da agogon hannu biyu. Sannan atisayen ya yi sanadiyyar raunata wasu sojoji huɗu da kuma lalata motar kariyar sojoji ta MRAP.

By Babaji

Leave a Reply