Gwamnatin Nasarawa ta rufe kasuwar tumatir ta Lafia

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Gwamnatin Jihar Nasarawa ta ba da umarnin rufe kasuwar tumatir ta Lafiya nan take saboda zargin rashin tsafta da matsalolin lafiyar jama’a.

Dakta Margaret Elayo kwamishiniyar ma’aikatar muhalli da albarkatun ƙasa ta ta rufe kasuwar ranar Asabar yayin duba sintirin na musamman don tsarkake muhalli na watan Agusta.

Ta bayyana cewa Gwamna Abdullahi Sule ya amince da a tsaftace kasuwar sosai kuma an yi hakan sau da yawa amma ta nuna rashin jin daɗin ta kan halin da ‘yan kasuwa ke nunawa.

Kwamishinan wacce ta jagoranci tawagar tilastawa, ta ce an rufe kasuwar ne bayan gargaɗi da dama da aka bai wa ‘yan kasuwa da masu gudanar da kasuwa kan su tsaftace muhallin.

“Mun lura da tarin shara, rashin magudanan ruwa, da rashin tsafta wajen sarrafa kayan abinci masu lalacewa cikin sauri a wannan kasuwa.
Wannan barazana ce ta lafiya ga mazauna jihar kuma gwamnati ba za ta zauna ba tare da ta ɗauki mataki ba ta bar masu halin ‘yan kasuwa su haifar da ɓarkewar cuta ba,” inji ta.

Elayo ta ƙara da cewa za a rufe kasuwar tsawon kwanaki biyu, Asabar da Lahadi, har sai ‘yan kasuwa da ƙungiyar kasuwa suka gudanar da cikakken aikin tsaftacewa da ya cika ƙa’idar tsafta ta ma’aikatar.

“Ma’aikatar za ta sake duba kasuwar ranar Litinin don ganin ko an yi tsaftacewar da ta dace da ƙa’idar muhalli kafin a buɗe kasuwar,” inji ta.

Hakazalika, kwamishinan ta ce tawagar tilastawa ta kama keke napep 37 a Lafiya saboda yin aiki cikin sa’o’in da aka keɓe don motsa jikin tsarkake muhalli.

Ta bayyana cewa za su ci gaba da riƙe keke napep ɗin na kwanaki biyu.

Ta ƙara da cewa ma’aikatar za ta gudanar da wani taro na wayar da kan masu keke napep a ranar Litinin daga ƙarfe 7:00 na safe zuwa 5:00 na yamma kafin a mayar masu da motocin.

Kwamishiniyar ta kuma yi kira ga jama’a da su riƙa kiyaye tsaftar muhallinsu domin kare kai daga ɓarkewar cututtuka.

“Idan muka kiyaye tsaftar muhalli, za mu kare kanmu daga yiwuwar ɓarkewar kowace cuta, kuma hakan zai tabbatar da ingantacciyar lafiyar jama’a,” inji ta.

Rahoton na wakilin mu ya ƙara da cewa kowacce ƙarshe Asabar na kowace wata gwamnatin jihar ta Nasarawa na gudanar da wannan sintirin domin
tsaftace muhallin jihar baki ɗaya.

By ukarofi

Leave a Reply