Ayatul Kursiyyu da DNA

Spread the love

Daga ALI ABUBAKAR SADIK

A kullum ci gaban kimiyya babu abinda ya ke yi sai dada nuna gaskiyar Ayoyin ƙurani da kalubalen da Allah ya tabbatar mana na cewa; ƙ41:53 “Zã Mu nũna musu ãyõyinMu a cikin sammai da kuma cikin halittarsu, har sai ya bayyana a gare su cẽwã lalle (Alƙur’ãni), gaskiya ne. Ashe, kuma Ubangijinka bai isa ba, ga cẽwa lalle Shĩ halartacce ne a kan kowane abu ne?”

A watan October na 2019, wani dakin binciken nazarin tsarin halitta Mai Rai na zahiri (Biophysics) da ke kasar Birtaniya sun sakin wani rahoton bincike a kan kwayoyin halittar gado (DNA) wanda ya nuna cewa ba kamar yadda ake tsammani ba tsawon shekaru daruruwa na binciken halittu masu Rai, musamman a kan kwayoyin halittar gado na DNA, cewar su na dauke ne da gado daga iyaye da kakanni zuwa yayansu, wato abin ya zarce nan domin wadannan kwayoyin halittar na gado su na aiki ne tamkar antenna Mai Rai, wato sashe ne da ke iya karbar bayanai daga waje ba kawai ya takaita daga sinadarai na cikin jiki ba. Kuma su na wannan aiki na karbar bayanai daga waje ta hanyar sararin maganadisun Duniya (Earth magnetic field) da cudanya da ma sauran sarari irin na lantar-maganadisu (electromagnetic fields).

A binciken na su, sun gano cewa daidaikun kwayoyin halittar gado (DNA) da aka ciro daga jiki na iya ta’ammali da sararin lantar-maganadisu (electromagnetic field) da ke waje, kuma su na tsayar da nuna wannan mu’amala da zarar an janye wannan lantar-maganadisu daga kusa da su. 
Babu wani abu, idan banda Rai kansa, wanda a cikin halittu masu Rai ke da matukar ban mamaki da gwaninta irin DNA, domin akwai kimanin Yan kanzagi (enzymes) guda 2000 da ake bukatar su jeru kafin samar da DNA, kuma tsautsayin (probability) su iya haduwa katsam (in random) sau guda daya, sai an gwada sau 10⁴⁰⁰⁰⁰. To an kiyasta cewa dukkan kwayar halitta (atoms) da ke cikin kaunu gaba daya guda 10⁸⁰ ne kacal. Akwai lambar googol wadda a lissafi ita ce kamar magaryar tukewa, 10¹⁰⁰, to ita kanta sai an ninka ta sau 400 za ta kamo waccan. Kada a manta fa muna maganar jera Yan kanzagi (enzymes) 2000 na DNA guda daya na halitta ba tare da mai saitawa ba sai an gwada sau waccan lambar. Tabbas babu yadda za’a yi wannan tsari ya zo katsam a lissafe.

Shi yasa wannan gagarumin nazari da su ka bayyana na cewa DNA ya na ta’ammali da sararin lantar-maganadisu ya tada hankalin mulhidai yadda cikin sauri sai aka wayi gari da cewa an rufe wannan dakin bincike da zummar za’a yiwa ginin kwaskwarima. A ka tsayar da ci gaban duk wani bincike a wurin kuma aka kwashe, tare da batar da duk wasu takardun bayanai na bincikensu.

Dalilin yin haka a bayyane ya ke, domin a wannan Duniya ta mu ta yau, mulhidai (Atheists) sun mamaye duk wata kafar kimiyya, bincike da ilimi. Kuma duk wani abu da ke kokarin nuna cewa akwai Allah, su na yaki da shi. Shi kuma wannan binciken idan aka dube shi da idon basira ya na tabbatar da cewa ikirarin kimiyyar Mulhidanci da ke nuna cewa babu wanda ya yi halitta, ita ta yi kanta ba gaskiya ba ne. Don haka duk wata hujja da zata nuna cewa akwai wani abu daga waje da ke juyawa da tsarawa ko kula da yadda halitta ke wanzuwa, ya rushe tsarinsu kuma ya tabbatar da ubangiji, don haka dole su yake shi. Shi yasa su ke da’awar cewa ai babu wani abu wai shi Rai (soul) ko consciousness daga waje. Komai ya samu ne sakamakon tsautsayi (randomness) kuma a makance (blind) karkashin sa’a (luck) ya ke tafiya, amma babu mai tafiyar da shi. Tsarin DNA ya wofintar da wannan ikirari.

To, ba wannan nazari kawai da su ka murkushe ba, akwai binciken Luc Montagnier wanda ya lashe gasar Nobel a 2008 kan nazarin kwayar cutar HIV, wanda ya wallafa bincikensa da ke nuna cewa hakika kwayoyin halittar gado na DNA, su na ta’ammali da lantar-maganadisu (a freƙuency na radio) a yayin cudanya da ruwa. Kuma wannan bincike dai ba za su iya danne shi ba saboda ya biyo ta layinsu.

A takaice abinda wadannan bincike ke nunawa shine cewa rayuwa na wanzuwa ne ba daga lullubar jiki kawai ba, ta na ta’ammali kai tsaye da abubuwa daga waje. Kuma idan har kwayoyin halittar gado na DNA na iya ta’ammali kai tsaye da lantar-maganadisu (electromagnetic fields), hakika wannan ya na tabbatar da cewa dukkan rayuwa na da alaka kuma zata kasance ba ta haihuwa kawai mu ke samuwa da wanzuwa ba, akwai yiwuwar wani makunni kamar na lantarki da zai iya kunna mu ya kashe mu. Wato DNA ba kawai gado ya ke sadarwa ba, domin idan ya kasance tamkar antenna mai ta’ammali da sararin lantar-maganadisu, ya zama mai karbar bayanai na wanzuwa. Hakan kuma na nuna akwai mai iya sarrafa shi daga waje.
Allah ya tunatar da mu cikin Ayatul ƙursiyu cewa; ƙ2:255 “Allah, bãbu wani Ubangiji fãce Shi, Rãyayye, Mai wanzar da kõmai, gyangyaɗi bã ya kãma Shi, kuma barci bã ya kãma Shi, Shi ne da abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa.”

Saboda haka shi Allah ba kawai yayi halitta ya ja gefe ba ne, a’a, shine mai tallafawa halittar ta ci gaba da wanzuwa ta hanyar tsaruka (natural process) wadanda ya shirya su bisa wasu dokoki (laws) wadanda dole halitta ta bi wannan tsari, ko ta na so ko ba ta so. Shine abinda ya ke nufi da ya ce; ƙ41:11 “Sa’an nan Ya daidaita zuwa ga sama alhãli kuwa ita (a lõkacin) hayãƙi ce, sai Ya ce mata, ita da ƙasã “Ku zo, bisa ga yarda kõ a kan tĩlas.” Suka ce: “Mun zo, munã mãsu ɗã’ã.”

Wato cikin ginshikan dokoki (laws) da ya dora tsarin duk wata halitta Mai jiki (matter) shine na saka maganadisu (gravity) ya zama jigon duk wani motsi (laws of motion). Kamar yadda bahaushe ke da maganar cewa “komai nisan jifa, kasa zai sauka”. Gravity ya zama dokar da duk wasu jikuna dole su ke biyayya gare ta “ko bisa yarda ko a kan tilas” kamar yadda ayar ta bayyana.

Babu wata halitta da ta tserewa tsarukan wanzuwar halitta (natural laws), kuma tsari ne wanda ya ke bai daya a cikin ilahirin kaunu (universe), wadda kasancewar hakan kadai na dada tabbatar da samuwar ubangiji. Kamar yadda Allah ya ce; ƙ54:49 “Lalle Mũ, kõwane irin abu Mun halitta shi a kan tsãri (laws).”

Domin babu yadda za’a yi Alloli kishiyoyin juna su wanzu a tare domin dole a sami sabanin ra’ayi da karfin Iko. Su kansu wadanda ke inkarin samuwar Allah sun tabbatar da cewa tsarin halitta na gudana akan wani tsari da Iko na bai-daya (naturalistic), kuma idan an tambaye su wanene ya yi halitta, duk da korewarsu ta ubangiji, sai su ce maka halitta ta samu ta wani tsari mai hikima, Iko da karfi wanda ke sarrafa kansa, wanda su ke baiwa lakabin “Nature” ko “Naturalistic”, wanda ba kowa ba ne illa dai Allah ubangiji wanda ba sa son su kira da ainihin sunansa. Kamar yadda Allah ya jaddada mana cikin; ƙ31:25 “Kuma lalle, idan ka tambaye su, “Wãne ne ya halĩtta sammai da kasa?” Lalle zã su ce: “Allah ne.”

Wato duk da bijirewa Allah da kore shi da mulhidai ke yi, a karshe dai wani abu mai siffofin Allah gaba daya, su ke nuna cewa dai shine mahaliccin. Wato Nature din da su ke ikirari za ka samu bata da banbanci da duk wasu attributes na Ubangiji. Wato ita ta samar da halitta, kuma ba ta da abokin tarayya, ita ke tafiyar da halitta yadda ta so, babu tsarin da zai ja da ita dss wato dai a takaice kawai sun kwace sunan Allah ne sun mayar a kan nature.

A ƙarshe sai Allah ya mana kalubale da kuma Jan hankali, kalubalen shine; ƙ22:73 “Ya ku mutãne! ga wani misãli, sai ku saurãra zuwa gare shi. Lalle ne waɗanda kuke kira baicin Allah, bã zã su halitta ƙudã ba, kõ da sun tãru gare shi gaba daya.”

Idan ka ce ba Allah ne mahalicci ba, to yi amfani da karfin Ilimin kimiyyar da kake takama da shi ka halicci kuda kawai, kuma ko da ba naka na daban ba, a’a , ka kwaikwayi irin irin na Allah amma sharadin shine ka samar da shi daga halitta mara Rai. 

Zan rufe wannan maƙalar da Jan hankalin da Allah ya yi mana cewa; ƙƙ21:22 “Dã waɗansu abũbuwan bautawa sun kasance a cikinsu (sama da ƙasa) bayan Allah, haƙĩƙa dã su biyun sun ɓãci. Sabõda haka tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin Al´arshi daga abin da suke siffantãwa.”

Malam Ali manazarci ne a Kano

By ukarofi