Shin dalolin IPOB za su kafa Biyafara?

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

’Yan awaren Biyafara da su ka samo asali ne daga gungun maciyin amana Chukwuma Nzeogwu da ya shekar da jinin Sardauna, na kashe dala dubu 66 duk wata ga kamfanin farafaganda a Washington don yayata labarun karya na ɓatanci ga Nijeriya a wajen shugaba Trump. ’Yan Biyafara na son Trump ya kara ɗaukar matakai masu tsauri kan takurawa Nijeriya sannan ya mara mu su baya su kafa ƙasar Biyafara. Ba ‘yan Biyafara kaɗai ke wannan sharrin ba, akwai wasu mutane ko ƙungiyoyi da ke ruruta labarun karya na wai a na kisan kare dangi kan mabiya addinin Kirista a Nijeriya. Duk ɗan Nijeriya mai adalci, kai ko marar adalci indai a Arewa ya ke ya san ikirarin tantagariyar karya ne daga mugayen mutane maƙiya zaman lafiya masu sha’awar zubar da jini.

Yayin da IPOB ke ingiza kamfen da bagaye wai Hausawa zalla a Arewa don tada fitinar mummunan yaƙin ƙabilanci, shin nawa ta ke kashewa duk wata wajen daukar nauyin yara ‘yan zaman kashe wando su wuni su kwana kan soshalmidiya da sunayen karya su na zagin Shehu Mujaddadi, yin mugun alkaba’i ga iyaye magabata Sir Ahmadu Bello da sauran manyan malaman musulunci? Duk sharar da su ka kwaso sai su lafta kan Musulunci. Chinasa Nworu na rediyon Biyafara ya fito karara ya nuna burin IPOB na wargaza Arewa ta zama ‘yan bukkokin mulkin ƙabilu da dawo da Biyafara. Nworu da ke kanbama ‘yan ƙungiyar karyar Hausa zalla, ya kan yi amfani da kalmomin ingizawa cewa “me ku ke jira” Gaskiya a nazarinmu sanya Arewa ta shiga ɗauki ba dadin ƙabilanci tsakanin Hausawa daga batun sauya manyan limaman masallatai da amfani da makamai na da burin da tun watan Disamba 2025 an gama hargitsa yankin.

Haba biri ya yi kama da mutum yadda marar sa aikin yi daga yankin ƙirƙira na bambancin addini Middle Belt ke kartar ƙasa da shiryawa kokuwar Arewa maƙarƙashiya. Akwai waɗanda ko ba a ba su komai ba za su iya fakewa da addinin Kirista da sam-sam ba sa bin koyarwar BIBLE don haddasa zubar da jini. A ina ne a BIBLE a ka amincewa matasa ‘yan barasa su tare hanya su kashe matafiya ko wani wulli ya ja zuga su dau makamai su yi ta kashe-kashe haka siddan wai kare yankinsa ya ke yi. IPOB sun yi ƙaurin suna wajen son kuɗi don haka ko a kan Biyafara sai sun ci moriyar daloli da turawa wakilansu a Arewa kasonsu don samun kayan aikin farafaganɗa. Lallai yaran karyar Hausa su rika titsiye manyan don kar a sha su masilla. Harkar dalar Amurka a ke yi.

Zafin sharrin da a ke yi wa Nijeriya ya sa gwamnatin tarayya ta shugaba Bola Ahmed Tinubu ɗaukar kamfanin gyara-suna DCI Group AZ, LLC don yaƙi da labarun kanzon kurege da a ke kai wa gwamnatin Trump a Washington. Duk wata gwamnati za ta biya dala dubu 750 na tsawon wata 6 a ga abun da Allah zai yi don ‘yan Biyafara sun rikice ainun da neman a matsa lamba su kafa ƙasarsu a kuma wargaza Arewa. Wallahi ko karo-karo a ke nema za mu riƙa yi don tara kuɗin da za a kare mutuncin Nijeriya a idon duniya.

Kwanakin baya mai ba wa shugaba Tinubu shawara kan tsaro Malam Nuhu Ribadu ya sauka a Washington ya gana da jami’an gwamnatin Trump ya yayyafa ruwan ƙanƙara kan gagarumin sharrin da maƙiya Nijeriya su ka ƙulla. Aƙalla an samu fahimtar juna na yin aiki tare kan lamuran tsaro da kuma amincewa da ba wanda a ke nunwa wariya wajen kulawa.

Duk miyagun iri su shafawa kansu ruwa tun kafin hukuma ta yi mu su dirar mikiya don ba ƙasar da za ta yi sako-sako da masu cin amana.

Ashe duk zaman da mu ke yi da waɗanda ba su kan tafarkin tauhidi dutse ne a hannun riga. In ka ji kalmar MUMU, MALO, ABOKI duk na niyyar izgili, ’yan kudu ke jifar Hausawa da sunayen. Wannan ya sa wasu ’yan Arewa wadanda ba Hausawa ba da su ka haifi ‘yan karyar Hausa zalla su ka rika ƙoƙarin cewa su ba Hausawa ba ne a kudu don samun karɓuwa. Abun takaici ko coci ‘yan Arewa su ka yi ƙoƙarin shiga a kudu maso gabar wajen Igbo korar su a ke yi don a na ganin ba su ma cancanci zama kirista ba. Kuma gaskiyar magana duk duniya ba Kiristoci mafiya zafi da su ka kai na Arewa. Matsalar kawai son addinin Kirista su ke yi amma ba sa bin koyarwar addinin sam-sam don akasarin su musamman masu hayaniya a soshalmidiya ba su san komai a BIBLE ba. Masu tare hanya a Gonin Gora su kashe mutane ba sa bin BIBLE sam. Masu kashe mutane matafiya a Filato, Kudancin Kaduna da sauransu ba sa amfani da BIBLE sai ƙabilancin da su ka ɓoye a kasan addini.

Tun zaɓen 2023 da Musulmi da Musulmi su ka yi takara a APC wanda haƙiƙa harkar ‘yan siyasa ne, zafin wannan kamfen ɗin na rusa Arewa ya kankama inda duk makiya Arewa su ka shiga nazarin ɓatagari da za su yi amfani da su don hargitsa yankin. ’Yan IPOB sun samu logar amfani da masu jin harshen Hausa a ƙananan ƙabilu su ka dau nauyinsu don zafafa kamfen ɗin batanci ga shugabannin Musulunci da su ka haɗa da malamai masu ba da shawara wanda su ke ganin ya dace a zaba a lokacin babban zaɓe. Matasan ƙananan ƙabilu masu zaman kashe wando ’yan ina-da-kisa sun samu sana’a a bulus ta wuni su na zagin Musulmi da fakewa da yaƙi da Fulani. Sun buɗe shafuka na karya ba sunan gaskiya ba hoto ba adireshi sai farafaganda marar tushe da babu ita a ƙasa sai kan yanar gizo da kafa tarkon zuga musulmi Hausawa, su hau yaki kawai daga masallatai ko lokacin zaɓe su ce su gara ma Igbo da ɗan Arewa.

Rashin sa’ar da mutanen nan su ka samu shi ne su dai tun da ba Musulunci ne addininsu ba, ba su fahimci ƙarfin addinin ya shafe duk wata dasisa ta ƙabilanci kuma ko da za a shekara 2000 a na yi ba mai ajiye addininsa ya zaɓi ƙabilanci ko ya koma sanya sarka da ɗan kunne a wuya kamar wasu matasan yankin ƙirƙira da ba ya tsarin siyasar ƙasa. Sun so yadda su ka mara baya ga Peter Obi a Leba a 2023 ya sake fitowa a irin wannan jam’iyyar maimakon watsa mu su kasa a ido da ya yi, ya haɗe da su Alhaji Atiku Abubakar a jam’iyyar ADC. Duk ƙoƙarin da Atiku ke yi na nuna shi ba ya nuna wariya kuma kowa ɗan Nijeriya na sa ne amma tun da ya na sallah to shi mugu ne Bafulatani ne kar a zaɓe shi.

Asalin zauna-gari banza da IPOB ke amfani da su a Arewa ba komai ba ne don ba ma wanda ya san su sai a fesbuk nan ma a ɓoye su ke don tunanin kar a cafke su wanda kuma buyan ba mai ɗorewa ba ne don an san su sarai. Wani madugun su ma da ya yi rejistar bogi na cikin firgici don ya san bai shuka alheri ba kuma zai iya cin karo da hushin hukuma don haka ya ke gararamba a Bompai ko zai samu masu cewa sun san da zaman sa.

Don makircin IPOB fa ta hana ‘yan karyar Hausa zalla yin Allah wadai ko da na makirci ne ga dirar miƙiya da ‘yan ta’addan jihar Edo su ka sake yi wa ‘yan kasuwa Hausawa su ka yi bidi-bidi da su da kashe mu su awakinsu da sace mu su sauran dabbobin da su ke sayarwa a kasuwar Ekpoma. Hakanan sun hana su sharhi kan mafarauta 16 da ‘yan ta’addan Uromi nan ma a jihar Edo su ka kashe. Sun hana su magana kan mahauta da ‘yan ta’addan IPOB/ESN ke kashewa a Owerri da sauran garuruwan kudu maso gabar. Aikin da su ka umurce su, su rika yi shi ne Turji ya yi kaza da kaza da kaza. Kuma ba sa son a kawo ƙarshen Turji sam-sam sai sun cimma burin amfani da fitinar ‘yan ta’addan daji wajen kammala wargaza Arewa su kafa ƙasar Biyafara su rika tinƙaho, su ke da man fetur. Su ma kananan makirai ne don Biyafara ba za ta yiwu ba in ma ta yiwu jihohin kudu maso kudu ba za su amince ba. Su ya su IPOB sun dinga hallaka juna kenan ta hanyar ƙungiyoyin ta’addancinsu irin ESN.

KAMMALAWA

Ba wawaye a mutanen nan irin Hausawan ƙarya don idan fitinar ta tashi za su rasa ‘yan uwa ba Kudu ba Arewa. Dama IPOB na ganinsu gaulaye kuma ba za ta shigar da su jama’arta ba don haushin akwai hafsoshin soja na yankin da su ka ƙirƙira MIDDLE BELT da ke cikin dakarun da su ka wargaza Biyafara. Nan kuma Arewa sun ci mutuncin al’umma. Wallahi Hausawan bogi ku shafawa kanku ruwa. Allah ya kai mu 2027 ɗin mu ga abun da Allah zai zaɓawa Nijeriya kuma tabbas ba zai yi wa miyagu daɗi ba. Kazalika na tabbata jami’an tsaro za su yi farautar masu ingiza fitinar nan su cafke su don fuskantar tuhumar cin amanar ƙasa. A na tara bayanai a kansu.

By ukarofi