Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Masana harkokin tsaro da shugabannin al’umma a Jihar Kwara sun bayyana ra’ayoyi mabambanta kan shirin ɗaukar jami’an tsaron gandun daji, domin kare yankunan da gwamnati ba ta da cikakken iko a kansu, a wani yunƙuri na daƙile matsalar rashin tsaro da ke ƙara ta’azzara a sassan Nijeriya.
Wani tsohon jami’in tallafa wa ayyukan ’yan sanda na al’umma a Birtaniya, ɗan asalin birnin Ilorin mai suina Taiwo Hanbali AbdulRaheem, ya bayyana cewa, ɗaukar jami’an tsaron gandun daji mataki ne mai kyau da ya dace a wannan lokaci.
Sai dai ya yi gargaɗin cewa jami’an ba su da isasshen ƙarfin da za su iya murƙushe ’yan bindiga, yana mai cewa makaman da ’yan bindigar ke amfani da su sun fi na wasu daga cikin jami’an tsaro na zamani ƙarfi.
AbdulRaheem ya ce ya kamata gwamnati ta rungumi fasahar zamani wajen yaƙi da miyagun laifuka, kamar yadda ake yi a ƙasashe irin su Birtaniya, Mali da Burkina Faso.
Ya ce, “Mataki ne mai kyau, amma ba zai warware matsalar tsaro gaba ɗaya ba. Abin da ake buƙata shi ne amfani da fasahohin zamani masu ƙarfi da za su rika bibiyar motsin ’yan bindiga. Muna buƙatar jiragen sama marasa matuƙa (drones) masu ƙarfi da za su iya sanya ido a kan dazuka da sauran wurare masu muhimmanci.
Ba lallai sojoji su shiga daji su yi artabu kai tsaye ba, ana iya amfani da waɗannan jirage wajen kai hare-hare kan miyagun laifuka. Idan aka dogara da jami’an tsaron daji kaɗai, ’yan bindiga za su iya kashe su. A Birtaniya ana amfani da diron wajen sa ido a dazuka. Haka kuma Burkina Faso da Mali suna amfani da irin wannan tsari.”
Shi ma wani tsohon babban jami’in rundunar ’yan sanda, Ajayi Okasanmi, ya ce shirin ɗaukar jami’an tsaron daji dubu ɗaya domin ƙarfafa tsarin tsaro abu ne mai kyau, amma da ya fi tasiri da an aiwatar da shi tun kafin hare-haren da ake fuskanta.
Ya kuma yi magana kan batun kafa ’yan sandan jihohi, yana mai cewa hakan na iya taimakawa wajen yaƙi da ta’addanci, amma ya zargi gwamnati da rashin ɗaukar matakan kariya tun da wuri.
“Ana buƙatar gwamnati ta fito fili ta bayyana yadda za a horas da jami’an, irin kayan aikin da za a ba su da kuma yadda za a kula da walwalarsu. Idan ba a yi hakan ba, manufar ba za ta cimma burinta ba,” inji shi.
A nasa ɓangaren, Mai Kula da ƙungiyar Sa-Idon Tsaro ta Haɗin Gwiwa a Kudancin Kwara, Olaitan Zubair, ya ce akwai buƙatar ƙara yawan jami’an tsaron daji, tare da mayar da hankali kan tantancewa da kula da dazuka yadda ya kamata.
Shi kuwa Babban Mataimaki na Musamman kan Harkokin Tsaro, Muhideen Aliyu, ya bayyana cewa gwamnati na haɗa kai da mafarauta da masu aikin sintiri na sa-kai wajen yaƙi da rashin tsaro.
Ya ce, shugabannin ƙananan hukumomi sun samu umarni da kuma damar kafa ƙungiyoyin tsaro na gwamnati a yankunansu, waɗanda za su yi aiki tare da hukumomin tsaro na gargajiya kamar rundunar soji da jami’an tsaron daji.
A cewarsa, an riga an fara gudanar da irin waɗannan shirye-shirye a ƙananan hukumomin Edu, Patigi, Moro, Offa, Oyun da kuma Ifelodun, inda ake ƙoƙarin kare al’umma daga barazanar masu aikata laifuka.
