Yadda ‘yan bindiga suka haska maƙudan kuɗaɗen fansar da suka karɓa a wani bidiyo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna yadda wasu ‘yan bindiga suke nuna wasu maƙudan kuɗaɗe da ake zargin na fansa ne da suka karɓa a hannun jama’a sakamakon garkuwa da makusantansu, lamarin da ya haifar da damuwa akan ƙamarin rashin tsaro a Nijeriya.

Sanannen ɗan jarida, Bakatsine, wanda ya shahara da ruwaito labaran rikici da rashin tsaro ne ya wallafa bidiyon a ranar Asabar.

Ɗan jaridar, wanda ya wallafa bidiyon ta kafar X, ya ce: “wannan bidiyon ya nuna ‘yan bindiga na baje kolin kuɗaɗen da aka samu ta biyan fansa. Allah ya kawo ƙarshen wannan abin takaicin da zaman lafiya mai ɗorewa ga Nijeriya.

A ‘yan shekarun nan dai ayyukan garkuwa da mutane da karɓar kuɗaɗen fansa sun zama ruwan dare musamman a sassan arewa maso yamma da arewa ta tsakiya, inda ‘yan bindiga ke cigaba da farmakar mutane a ƙauyuka, matafiya, makarantu da kuma manoma.

Haka kuma, ‘yan bindigar sun faɗaɗa ayyukansu zuwa wasu sassan kudancin ƙasar, inda suke garkuwa da mazauna, matafiya da ma halaka wasu duk da biyan kuɗin fansa.

By Babaji

Leave a Reply