ISIS ta fitar da bidiyon babban rumbun makaman sojoji da ta ƙwace a Nijar

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta da ƙungiyar ISIS ta wallafa bayan wani mummunan hari a sansanin sojojin Jamhuriyar Nijar a yankin Inates, inda aka nuna wani babban rumbum makaman sojoji da aka ƙwace yayin samamen.

A ranar Lahadi ne ɗan jarida da ya shahara wajen yaɗa labaran ayyukan ‘yan ta’adda, Bakatsine, ya wallafa bidiyon da ke nuna manyan makaman daga rumbun sojin.

Saidai a yayin haɗa wannan rahoto, ba a kai ga tabbatar da sahihancin bidiyon ba da kuma adadin makaman da aka haska.

A cewar ɗan jaridar, al’amarin ya haifar da sabon damuwa akan yadda ƙungiyoyin ‘yan ta’adda da ke ayyukansu a yankin Sahel suke ƙara ƙarfi, inda ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi suke ƙaddamar da hare-harensu akan sojoji.

By Babaji

Leave a Reply