
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya NAHCON, ta nuna damuwa bisa ayyukan wasu ɓata-gari da ke yi mata sojan-gona wajen damfarar mutane ta hanyar karɓar kuɗaɗe daga masu aikin jigila da maniyyata da sunan samun kujerar Hajjin 2027 kai-tsaye.
A wata sanarwa da ta fitar a Abuja a ranar Lahadi, NAHCON ta yi gargaɗin cewa babu wani mutum, wakili, jami’in jigila ko ɗan shiga tsakani da ta amince wa karɓar kuɗi, kuɗin wakilci ko ƙarin wani kuɗi don mallaka, tabbatarwa ko bayar da kujerun hajji.
Hukumar ta ce, ana gudanar da aikin raba kujeru ne bisa biyayya ga sharuɗɗa da dokokin gudanarwar bayar da lasisi da ayyukan masu harkar jigilar hajji.
Ta kuma bayyana dukkan waɗanda ke karɓar kuɗi a hannun jama’a da sunan samar musu da kujerun Hajjin a matsayin masu aiki ta haramtacciyar hanya wadda babu sahalewarta aciki, tana mai kira ga al’umma da su kai ƙarar dukkan wanda aka samu yana aikata irin haka ga ‘yan sanda ko wata hukuma mai ruwa da tsaki akan haka.
Kazalika, NAHCON ta shawarci maniyyata da su biya kuɗin zuwa aikin hajji ta hanyoyin da ta amince da su, waɗanda suka haɗa da hukumomin jigilar alhazan jihohi, bankunan da take hulɗa da su da kuma masu aikin jigila da suke da lasisin aiki, tana mai kira ga jama’a da su ƙaurace wa dukkan wasu kiraye-kirayen waya, tura saƙonni da kuma neman biyan ƙarin wani kuɗi kan wanda ta ƙayyade da kuma dogara da samun labarai daga NAHCON da wasu hukumomin hajji.
A ƙarshe, ta tunatar da masu ruwa da tsaki da cewa za a ƙwace kujerun maniyyata matuƙar ba a shigar da bayanansu ba zuwa ranar 26 ga Satumba, 2026, yayin da za a tabbatar da kammala biyan kuɗaɗe zuwa ranar 2 ga Disambar 2026.
