Da Ɗumi-Ɗumi: Arsenal ta lashe Community Shield na 2026 bayan lallasa City

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal ta yi nasarar lashe kyautar wasan Community Shield na 2026 bayan casa Manchester City da ci 3 da 0 a Cardiff, Babban Birnin ƙasar Wales.

Hakan na zuwa ne ƙasa da mako guda da fara wasannin sabuwar kakar wasa ta gasar Premier League ta Birtaniya kuma ta 2026/2025.

Ɗan wasa Riccardo Calafiori ne ya ba wa Arsenal damar jan ragamar wasan bayan ƙasa da minti ɗaya da take wasan a lokacin da Lewis Skelly ya gara masa ƙwallo cikin salo mai ban ƙaye.

Ana tsaka da wasan ne a minti na 28, Kai Havartz na Jamus ya zura ƙwallo ta biyu da kai ta hannun sabon ɗan wasan gefe Cristos Tzolis, lamarin da ya ba wa Arsenal ƙwarin-gwiwar samu nasara a wasan.

Bayan an shafe mintina uku da koma wa hutun raɓin lokaci ne Kyaftin ɗin ƙungiyar ta arewacin Landon, Martin Ordergard ya zura ƙwallo ta ƙarshe.

A shekarar 2014 ne Manchester City ta sha kaye a irin wasan a hannun Arsenal da ci 3 da nema. Haka ma a 2023, inda aka tashi 1 da 1 kuma Arsenal ta yi nasara a bugun fenarati.

By Babaji

Leave a Reply