
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Lahadi tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i shigar da sabuwar ƙara akan Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ICPC, inda ya nemi a biya shi diyyar Naira biliyan 10.
El-Rufa’i ya yi ƙorafin ne akan ICPC bisa zargin ta da hana shi ganawa da matarsa, Aichatou Asabe; da ɗansa, Abba El-Rufa’i yayin da yake tsare.
A ƙarar, wadda lauyansa, Ubong Akpan ya shigar, El-Rufa’i ya zayyano shugaban ICPC da Antoni Janar na Ƙasa (AGF) a matsayin waɗanda aka shigar ƙara na biyu da na uku.
Tsararren tsohon gwamnan, wanda ya yi zargin an hana matarsa da ɗansa ganin sa, ya nemi kotu ta biya masa buƙatu guda tara a ƙarar mai ɗauke da lambar FHC/ABJ/CS/1852/2026.
Daga ciki ya nemi kotun ta ayyana cewa ‘yancin ɗan-adam da dokar ƙasa ta 1999 ta ba shi yana cigaba da aiki kuma ba tare da la’akari da halin tsarewa da yake ciki ba.
Haka kuma, ya roƙi ta ayyana cewa haramta wa iyalan nasa zuwa ganin sa musamman don kai masa abinci, ba shi kulawar lafiya da wasu buƙatu ba tare da wani izinin doka ba, tauye masa ‘yanci ne. Ya kuma kafa hujja da cewa, yana da ‘yancin samun dukkan waɗannan ababe da yake buƙata kamar yadda sashe na 34 da na 37 na Dokar ƙasa da Sashe na 5 da na 18 na Dokokin ‘yancin Ɗan-adam da Al’umma na Afirka suka tanada.
Sannan, tsohon gwamnan ya buƙaci kotun da ta ayyana hana ganin sa, wulaƙanci da rashin mutuntawa da ya yi zargin jami’an ICPC sun yi wa Asaba da Abba a ranar 7 ga Yuli da kuma shiga tsakanin iyalai da alaƙarsu, tauye ‘yancin kare mutuncin ɗan-adam da rayuwarsa ta kai-da-kai da ta iyali ne.
Don haka ya nemi kotun ta ba wa ɓangarorin da ya shigar ƙarar umarnin ƙyale shi ganawa da iyalansa a baki ɗaya lokacin da yake tsare kamar yadda Babbar Kotun Tarayya ta bayar da umarni da fari.
