
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya Gwamna Ademola Adeleke na Osun murna bayan sake samun nasara a zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar a jiya Asabar, yayin da ‘yan ɓangaren adawa su Atiku Abubakar da Peter Obi suka bayyana sakamakon a matsayin tasirin zaɓin masu zaɓen jihar.
Adeleke ya samu nasarar ne bayan samun ƙuri’a 511,067, yayin da Oyebamiji ya samu 444,815. Najeem Salaam na ADC ya samu 17,180 a zaɓen, wanda aka gudanar a faɗin ƙananan hukumomi 30 na jihar.
Gwamnan ya shiga zaɓen ne a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar Accord Party bayan ficewa daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP.
A jawabinsa, Adeleke ya jinina wa Shugaba Tinubu bisa barin harkokin zaɓe su tafi yadda aka tsara ba tare da tsoma baki ba, duk da cewa ya yi iƙirarin ba za a kira zaɓen ba da sahihi baki ɗayansa saboda zargin kame da matsa wa magoya bayan ‘yan ɓangaren adawa.
A ɗaya ɓangaren kuwa, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a zaɓen 2027, Atiku Abubakar ya ce ‘yan jihar sun yi amfani da ‘yancin da dokar ƙasa da dimukraɗiyya ta ba su na su zaɓi wanda suke so, don haka ya taya Adeleke murnar nasarar sake zama gwamnan jihar.
Ya kuma yaba wa masu zaɓe bisa yadda suka yi tururuwa wajen kaɗa ƙuri’asu yayin zaɓen, kamar yadda aka wallafa a sahihin shafinsa na sada zumunta.
Shi ma Peter Obi na jam’iyyar NDC ya taya Adeleke murnar lashe zaɓen tare da al’ummar jihar, inda ya ce al’ummar sun yanke hukuncin wanda zai jagorance su bisa ‘yancin dokar ƙasa da kuma yaba wa matasa masu zaɓe a jihar kan abin da ya kira da sanya ido wajen bayar da kariya ga ƙuri’unsu.
