Koriya ta Arewa ta harba makami mai linzami gabanin atisayen sojojin Amurka da na Koriya ta Kudu

Spread the love

Koriya ta Arewa ta harba wani makami mai linzami zuwa tekun da ke gabashin yankin Koriya, kwanaki kaɗan kafin Amurka da Koriya ta Kudu su fara wani babban atisayen soji na haɗin gwiwa.

Hukumomin tsaron Koriya ta Kudu da Japan ne suka tabbatar da harba makamin, wanda aka harba daga yankin Wonsan da misalin karfe 6 na safiyar Laraba.

Makamin ya yi tafiyar kusan kilomita 700 kafin ya faɗa cikin teku, a cewar hukumomin ƙasashen biyu.

Wannan shi ne karo na biyu cikin kwanaki shida da Koriya ta Arewa ta harba makami daga yankin Wonsan, bayan harba wani makamin a ranar 6 ga watan Agusta.

Har yanzu hukumomin Koriya ta Kudu ba su bayyana takamaiman nau’in makamin da aka harba ba, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan yanayinsa da yadda ya yi tafiya.

Wani babban mai bincike a Cibiyar Nazarin Hadin Kan Koriya da ke Seoul, Hong Min, ya ce mai yiwuwa harba makamin wani ɓangare ne na shirin bunƙasa makaman Koriya ta Arewa, amma ba za a yi watsi da yiwuwar cewa lokacin da aka harba shi an zaɓe shi ne domin aika saƙo gabanin atisayen sojin ba.

Amurka da Koriya ta Kudu za su gudanar da atisayen Ulchi Freedom Shield daga ranar 17 zuwa 27 ga watan Agusta. Atisayen zai mayar da hankali kan yadda ƙasashen biyu za su tunkari barazanar da Koriya ta Arewa ke haifarwa, ciki har da amfani da jirage marasa matuƙa, katse siginar GPS da hare-haren yanar gizo.

Koriya ta Arewa ta daɗe tana kallon irin waɗannan atisaye a matsayin barazana gare ta, yayin da Amurka da Koriya ta Kudu ke cewa manufarsu ita ce ƙarfafa shirinsu na kare Koriya ta Kudu.

A nata ɓangaren, ofishin tsaron Koriya ta Kudu ya gudanar da taron gaggawa tare da bayyana damuwarsa kan ci gaba da harba makamai da Pyongyang ke yi.

Sojojin Koriya ta Kudu sun kuma ce suna cikin shirin ko-ta-kwana domin mayar da martani ga duk wani abin da za su dauka a matsayin barazana.

Sai dai rundunar sojin Amurka da ke yankin Indo-Pacific ta ce bincikenta na farko ya nuna cewa harbar makamin bai haifar da wata barazana ta gaggawa ga sojojin Amurka ko yankunanta, ko kuma kawayenta ba.

By ukarofi

Leave a Reply