Cire tallafin mai ya ceci Nijeriya daga nauyin tiriliyan N53 — Shugaban NRS

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Hukumar Haraji ta Nijeriya (NRS), Zacch Adedeji, ya bayyana cire tallafin man fetur a matsayin ɗaya daga cikin mafi kyawun matakan da aka taɓa ɗauka a tarihin tattalin arzikin Nijeriya, yana mai cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cancanci yabo saboda jajircewarsa wajen aiwatar da matakin.

Adedeji ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman da aka yi da shi a shirin Sunday Politics na gidan talabijin na Channels, inda ya kare sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin Tinubu tare da cewa wasu daga cikin nasarorin da ake gani a halin yanzu sun samo asali ne daga cire tallafin man fetur.

A cewarsa, tsarin tallafin man fetur ya daɗe yana zama babban nauyi ga tattalin arzikin ƙasa, kuma ba shi da ɗorewa, duk da cewa an ci gaba da aiwatar da shi tsawon shekaru.

“Dukkan kyawawan sakamakon da zan lissafa nan gaba sun samo asali ne daga wannan mataki na jarumta na cire tallafin man fetur. Don haka, ba kuskure ba ne; shi ne mafi kyawun abin da ya taɓa faruwa da wannan ƙasa. Tallafin ya kasance mugun abu kuma ya shafe shekaru da dama yana damun Nijeriya,” inji shi.

Shugaban NRS ya ce Shugaba Tinubu ya gaji tattalin arzikin da ke fama da tsarin tallafin man fetur wanda ba shi da ɗorewa, ɓangaren mai da ke kasa cika abin da ake tsammani daga gare shi, da kuma ƙarancin tushen samun haraji.

Ya ce gwamnatin ta ɗauki muhimman matakai domin magance waɗannan matsaloli na tsarin tattalin arzikin ƙasar.

Adedeji ya kuma yi watsi da sukar da ake yi wa sauye-sauyen, yana mai cewa bai kamata a riƙa tantance manufofin tattalin arziki bisa son rai ko motsin rai ba, domin ana buƙatar sauye-sauyen ne domin sake gina tattalin arzikin ƙasar kan tubalin da zai iya ɗorewa.

Ya kuma ƙalubalanci masu neman shugabancin ƙasa a 2027 da su bayyana abin da za su yi daban idan aka kwatanta da manufofin gwamnatin Tinubu.

“Abin da Shugaban ƙasa ya cancanta da shi yanzu shi ne goyon baya da yabo saboda ya nuna kansa ɗan ƙasa mai kishin ƙasa ne, ba ɗan siyasa kawai ba. Duk wanda ya ce zai zo ya yi takara, a tambaye shi: ‘Me za ka yi daban?’ Shin suna cewa cire tallafin man fetur kuskure ne? Shin suna cewa haɗa farashin canjin kuɗi kuskure ne?” inji Adedeji.

Adedeji ya ce da Nijeriya ta ci gaba da tsarin tallafin man fetur, kuɗin tallafin ka iya kaiwa kusan tiriliyan N53, yayin da darajar naira a kan dala ka iya kaiwa kusan N3,500 kan dala ɗaya, musamman sakamakon sauye-sauyen da ke faruwa a kasuwar makamashi ta duniya da rikicin Iran.

Shugaba Tinubu ne ya sanar da cire tallafin man fetur a jawabinsa na rantsar da shi a ranar 29 ga Mayu, 2023. Matakin ya haifar da tashin farashin fetur, wanda daga bisani ya ƙara tsadar sufuri, abinci da kuma samar da kayayyaki.

Sai dai a gefe guda, sauyin ya taimaka wajen ƙara yawan kuɗaɗen shiga gwamnati da kuma kuɗaɗen da ake rabawa tsakanin matakan gwamnati uku ta asusun tarayya.

Yayin da yake magana kan matsin tattalin arziki da talauci da ƙarancin kuɗin shiga da iyalai ke fuskanta, Adedeji ya ce Hukumar Harajin Nijeriya ba a kafa ta domin wawure kuɗin ’yan ƙasa masu fama da ƙuncin rayuwa ba.

Ya ce manufar gwamnatin ita ce ta “haraji arziki, ba haraji talauci ba. Ba mu nan domin kwashe kuɗi, kuma wannan ita ce manufar Shugaban ƙasa. A gaskiya, abin da muke mayar da hankali a kai ba kawai samun kuɗin shiga ba ne. Shugaban ƙasa ya sha cewa ni aikin da aka ba ni shi ne in haraji arziki. Ba na son in haraji talauci. Ina son in haraji amfanin gona, ba iri ba; ina son in haraji ribar zuba jari, ba jarin kansa ba.”

Ya bayyana cewa idan kamfanoni da ’yan kasuwa suka bunƙasa, kuɗaɗen harajin da gwamnati ke samu ma za su ƙaru.

“Idan kasuwanci ya yi kyau, kuɗaɗen shiga na Nijeriya za su yi kyau. Don haka ba aikinmu ba ne mu matsa wa mutane mu karɓi kuɗi. Shi ya sa aikinmu ya fi karkata wajen ganin kasuwanci yana bunƙasa,” inji shi.

Adedeji ya yi misali da cewa idan mutum ya samu naira 100, gwamnati za ta karɓi naira 30 a matsayin haraji; idan ya samu naira 200, za ta karɓi naira 60; idan kuma ya samu naira 300, harajin zai kai naira 90.

Saboda haka, ya ce idan hukumar na son ƙara yawan kuɗaɗen haraji, wajibi ne ta taimaka wajen samar da yanayin da zai ba ’yan kasuwa damar ƙara samun kuɗi. Ya danganta wasu daga cikin sauye-sauyen gwamnatin da ƙoƙarin kawar da matsalolin da ke hana kasuwanci bunƙasa, ciki har da sauye-sauye a ɓangaren wutar lantarki da kuma ƙarin rabon kuɗaɗe ga gwamnatocin jihohi. Ya ce, gwamnatocin jihohi suna da muhimmiyar rawa wajen rage talauci saboda kusancinsu da jama’a, musamman a fannonin ilimin firamare da sakandare.

By ukarofi

Leave a Reply