Yadda aka yi maulidin Sheikh Ahmadu Tijjani na 2026 ƙarƙashin Khalifa Ibrahim Dahiru Bauchi a Kano

Spread the love

Daga BILKISU YUSUF ALI a Kano

An gudanar da babban taron maulidin Sheikh Ahmad Tijjani a birnin Kano, wanda gidauniyar Sheikh Dahiru Usman Bauchi Foundation ta saba shiryawa duk shekara don tunawa da ranar haihuwar Shehi Ahmadu Tijjani da irin gudummawar da ya bayar wajen yaɗa addinin Musulunci da ɗariƙar Tijjaniyya a duniya. Taron ya kasance babban taro na addini mai ɗauke da tarihi da muhimmanci ga al’ummar Musulmi, musamman mabiya ɗariƙar Tijjaniyya. 

Taron, wata muhimmiyar dama ta tunatarwa da ilimintarwa da ƙarfafa zumunci tsakanin al’ummar Musulmi. Haka kuma, ya sake tabbatar da matsayi da muhimmancin birnin Kano a matsayin ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin ilimin addinin Musulunci da harkar Tijjaniyya a yankin Afirka ta Yamma. An fara ranar 5 zuwa 9 ga Agusta, 2026. 

Makon Shehu:

A yayin taron da aka gudanar daga ranar Laraba zuwa ranar Juma’a, malamai daban-daban sun gabatar da wa’azuzzuka, darussa da bayanai masu muhimmanci da suka shafi tarihin Sheikh Ahmad Tijjani, rayuwarsa da koyarwarsa da kuma gudunmawar da ya bayar wajen yaɗa ilimin addinin Musulunci. 

Malaman sun kuma yi kira ga mabiya ɗariƙar Tijjaniyya da sauran Musulmi baki ɗaya da su ƙara himma wajen neman ilimi da karatu da fahimtar addini. Saboda ɗariƙar Tijjaniyya ɗariƙa ce ta masu ilimi don haka ake ake ma kiran ɗariƙar da ɗariƙatu ahlil ilmi. 

Saukar Alƙur’ani na Sheikh ɗahiru Bauchi Foundation da cikar makarantar shekara 25:

Bayan kammala tarukan nakon Shehu sai kuma asabar aka yi taron yaye ɗalibai da bikin cika shekara 25 na makarantar Al-ƙur’ani ta Usman Bauchi Foundation a Kano. Yayin wannan taro, an gabatar da wasu daga cikin ɗaliban makarantar da suka yi fice wajen haddar Al-ƙur’ani. 

Daga cikin abin da ya ja hankalin mahalarta akwai yara guda biyu da suka yi nasarar haddace Al-ƙur’ani tun suna shekara sha biyar da sha biyu. Taron ya haɗa tsofaffin ɗaliban makarantar da zuriyar Sheikh ɗahiru Usman Bauchi da manyan mutane daga Kano da wajen Kano da baƙi daga ƙasashe daban-daban. 

Babban maulidin ranar Lahadi:

A ranar Lahadi ne aka gudanar da babban taron Maulidin Sheikh Ahmad Tijjani wanda ya kasance babban taron da ya tattaro manyan malamai da shugabannin Tijjaniyya na duniya akwai Sheikh Mahi Niass khalifan Sheikh Ibrahim daga Senegal sai Khalifan Tijjaniyya na duniya Khalifatul Am Sheikh Sidi Ali Bel Arabi daga Algeria da Masar da Palasɗine da Chadi da Kwatano da Morocco da Nijar da Togo da Ghana da Kamaru da Gambiya da sauran ƙasashe daban-daban har guda goma sha biyar. 

Taron ya kuma kasance wata dama ta jaddada cewa haɗin kan al’umma, da neman ilimi da girmama juna na daga cikin muhimman abubuwan da za su taimaka wajen ci gaban Musulmi. A gida Nijeriya kuwa ba za a iya tantance yawan manyan mutanen da suka halarta ba malamai da sarakai da masu riƙe da muƙamai a ƙasar. 

An gudanar da taron ne ƙarƙashin jagorancin Halifa Sheikh Ibrahim Sheikh ɗahiru Usman Bauchi wanda shugaban ƙasar Nijeriya ya turo wakilcin sakataren ƙasa Mr Goarge Okume inda ya zo da ministoci shida. Ya isar da saƙon shugaban ƙasar Nijeriya ga mahalarta taron. 

Haka ita ma gwamnatin jihar Kano ta zo ƙarƙashin wakilcin mataimakin gwamnan jihar Kano Alhaji Murtala Sulen Garo inda ya nuna farin cikinsa ga wannan taron. An gudanar da taron a fadar Sarkin Kano na Nassarawa Alhaji Aminu Ado Bayero wanda ya zama uba a wannan mauludi. 

Mauludin da dukkan tarurrukan sun gudana ƙarƙashin jagorancin shugaban kwamiti Dr Lawi Sheikh Atiku Sanka da sakatarensa Dr Abubakar Maɗatai. An yi taro lafiya an kammala lafiya.

By ukarofi

Leave a Reply