
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An sanar da Ademola Adeleke a matsayin wanda ya yi nasara a mazaɓarsa ta 009 da ke Abogunde/Sagba a Ƙaramar Hukumar Ede ta Arewa a zaɓen gwamnan Jihar Osun da aka gudanar ranar Asabar.
A cewar sakamakon da malamar zaɓen yankin, Adebimpe Susan Dunsin ta sanar, Adeleke, wanda shi ne ɗan takarar jam’iyyar Accord Party kuma gwamna mai ci, ya samu ƙuri’a 421, wanda hakan ya sa ya yi nasarar kan sauran abokan karawarsa
Ɗan takarar jam’iyyar mai mulki APC, Bola Oyebamiji, ya samu ƙura 29 kacal, yayin da na ADC, Najeem Salaam ya samu ƙuri’a guda.
Wannan ya sanya magoya bayan Gwamna Adeleke sun taru wajen nuna murnarsu a fili ga nasarar da ɗan takarar nasu ya samu wajen rera waƙar “Imole”.
A jimillance, Ademola Adeleke, ya samu gagarumar nasara a ƙaramar hukumar, inda ya doke Bola Oyebamiji, da tazarar ƙuri’u 25,144.
Sakamakon da aka sanar a cibiyar tattara sakamakon zaɓen Ede ta Arewa ya nuna cewa Adeleke ya samu kuri’u 35,427, yayin da Oyebamiji ya samu 10,283.
Sai dai sakamakon da aka tattara a matakin ƙananan hukumomi har yanzu yana ƙarƙashin amincewar babban jami’in tattara sakamakon zaɓen na INEC, wanda zai gudanar da tattara sakamakon ƙarshe a Osogbo, babban birnin jihar yayin da aka kammala aikin haɗawa.
