Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Matatar Mai ta Dangote ta ƙara ƙarfafa matsayinta a kasuwar makamashi ta duniya bayan da ta sake zama mafi girman mai samar da man jiragen sama ga nahiyar Turai na wata na biyu a jere, inda ta sake zarce Amurka wajen yawan kayayyakin da ake shigowa da su.
A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Alhamis, ya bayyana cewa wannan nasarar ta sake tabbatar da irin tasirin da matatar ke ƙara samu a kasuwannin makamashi na duniya.
Kamfanin ya ce, bayanan shigo da man jiragen sama na Turai, waɗanda kamfanin binciken kasuwar kayayyaki na duniya, Kpler, ya tattara, sun nuna cewa sama da tan 400,000 na man jiragen sama da aka tace a matatar Dangote ne aka kai Turai a watan Yuli.
Adadin ya kai kusan kashi 20 cikin 100 na dukkan man jiragen sama da Turai ta shigo da shi a cikin watan.
Kamfanin ya ce, wannan ya biyo bayan wani sabon tarihi da aka kafa a watan Yuni, lokacin da aka fitar da tan 466,000 zuwa Turai, wanda a karon farko ya sa Nijeriya ta kwace wa Amurka matsayin babbar ƙasar da ke samar wa Turai man jiragen sama da ake shigowa da shi.
Sanarwar ta ce, ci gaba da samun wannan nasara ya nuna cewa matatar Dangote na iya samar da man jiragen sama mai inganci wanda ya cika ƙa’idodin ƙasashen duniya, duk da cewa kasuwar Turai na cikin mafi tsauraran kasuwannin makamashi a duniya.
Rahoton ya nuna cewa Turai ta shigo da kusan tan miliyan 2.06 na man jiragen sama a watan Yuli, inda matatar Dangote ta kasance mafi girman mai samar da wannan man fiye da masu fitar da shi daga Amurka da ƙasashen Gabas ta Tsakiya.
Kamfanin ya bayyana cewa matsayinsa ya samo asali ne daga kyakkyawan wurin da matatar take a gabar Tekun Atlantika, da kuma amfani da sabbin fasahohi, ƙarfin samarwa da kuma ingantaccen tsarin fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje.
Haka kuma, ya ce ƙaruwar samar da kayayyaki ce ta taimaka wajen bunƙasa fitar da man. A cewarsa, yawan man jiragen sama da aka ɗora domin fitarwa daga tashar Lekki ya kai sabon tarihi na tan 550,000 a watan Yuni, yayin da yawan ɗanyen man da ake kai wa matatar ya haura ganga 660,000 a kullum, lamarin da ya ba ta damar ƙara tacewa da fitar da kayayyakin man fetur zuwa kasuwannin duniya.
Matatar ta kuma bayyana cewa sauye-sauyen da ke faruwa a kasuwar makamashi ta duniya sun taimaka mata wajen ƙara samun kasuwa. Ta ce, duk da cewa Turai ta samu wasu ƙananan kayayyakin man jiragen sama daga Kuwait da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Oman a watan Yuli, rikice-rikicen da suka shafi mashigin Hormuz da kuma sauye-sauyen siyasa a duniya sun sa masu saye suka fara neman sabbin hanyoyin samun kayayyaki.
A sakamakon haka, matatar Dangote ta zama amintacciyar kuma gasa mai ƙarfi wajen samar da man jiragen sama, abin da ke ƙara nuna muhimmancin Nijeriya a harkokin cinikin tatattun kayayyakin man fetur na duniya.
Babban Jami’in Gudanarwa na Matatar Dangote, David Bird, ya ce baya ga man jiragen sama, kamfanin na ci gaba da fitar da dizal, fetur da sauran tatattun kayayyakin man fetur zuwa ƙasashen Turai, Afirka da sauran sassan duniya. Ya ce, wannan ci gaban ya ƙara tabbatar da matsayin Nijeriya a matsayin ƙasar da ke fitar da tatattun kayayyakin man fetur masu ƙima zuwa kasuwannin duniya.
