Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Sarkin Dutse na Jihar Jigawa, Dr Hameem Nuhu Sanusi, ya nuna damuwa kan yadda wasu mutanen da ba su da cikakken horo ko ƙwarewar aikin jarida ke kutsawa cikin sana’ar, yana mai cewa ayyukansu na lalata martabar aikin jarida.
Sarkin ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin Shugaban ƙungiyar ’Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ), Kwamared Alhassan Yahaya, tare da mambobin Majalisar Zartarwa ta ƙasa (NEC) ta ƙungiyar, waɗanda suka kai masa ziyarar ban girma a fadarsa da ke Dutse.
Tawagar NUJ ta je Dutse ne domin halartar taron NEC na ƙungiyar da ake gudanarwa duk bayan wata uku, wanda reshen NUJ na Jihar Jigawa ya karɓi baƙunci.
Sarkin ya ce abin takaici ne yadda wasu marasa ƙwarewa suka shiga aikin jarida, suna yaɗa labaran ƙarya, gurbatattu ko kuma marasa daidaito, lamarin da yake kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin al’umma.
Ya shawarci shugaban NUJ na ƙasa da ya kafa wani kwamiti mai ƙarfi da zai binciki tare da gano mutanen da suka cancanci a kawar da su daga sana’ar, domin tsaftace aikin jarida da dawo da martabarsa.
Sarkin ya ce ya kamata a ɗauki matakin ne saboda aikin jarida na da muhimmiyar rawa wajen gina dimokuraɗiyya mai ɗorewa.
A cewarsa, a matsayin abin da ake kira “rukuni na huɗu na gwamnati” a tsarin dimokuraɗiyya, NUJ da kafafen yaɗa labarai na iya taimakawa wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya ko kuma su zama sanadin raunana ta.
Ya ƙara da cewa, fadar Dutse tana bai wa aikin jarida muhimmanci sosai, har ta ɗora wani ƙwararren ɗan jarida mai dogon tarihi a cikin sana’ar a matsayin ɗaya daga cikin mambobin Majalisar Masarautar Dutse.
Tun da farko, Shugaban NUJ na ƙasa, Kwamared Alhassan Yahaya Abdullahi, ya ce tawagar ta kai ziyara fadar ne domin nuna girmamawa ga Sarkin Dutse, wanda ya ce ya daɗe yana bayar da goyon baya ga ƙungiyar, ba a Jigawa kaɗai ba har ma a matakin ƙasa, kamar yadda mahaifinsa marigayi ya yi a baya.
Alhassan ya ce sarakunan gargajiya, a matsayinsu na masu kula da zaman lafiya da haɗin kan al’umma, suna da muhimmiyar rawa wajen ba NUJ shawarwari da jagoranci domin samun kyakkyawan sakamako.
Daga bisani, shugaban NUJ na ƙasa tare da shugaban reshen NUJ na Jigawa mai masaukin baki, Kwamared Ismail Ibrahim Dutse, sun karrama Sarkin Dutse da lambar yabo ta girmamawa ta Patron na NUJ ta Jihar Jigawa.
Bayan kammala ziyarar, shugabannin NUJ na ƙasa sun zagaya domin duba wasu ayyukan noma, ilimi, hanyoyi da shirye-shiryen tallafa wa jama’a da gwamnatin Gwamna Umar Namadi ta aiwatar a jihar.
A yayin wannan ziyarar ta kwanaki uku, ana kuma sa ran Shugaban NUJ na ƙasa zai gana da mambobin Kwamitin Tsofaffin ’Yan Jarida (Veterans Committee) na NUJ reshen Jihar Jigawa.
