Tsohon dan damben Puerto Rico, Prichard Colón, ya rasu yana da shekaru 33, kusan shekaru 11 bayan wani mummunan faɗa da ya janyo masa zubar jini a kwakwalwa. Colón ya rasu ne ranar Alhamis, 13 ga Agusta, 2026, bayan ya shafe tsawon lokaci cikin wani yanayi na rashin cikakken sanin abin da ke faruwa a jikinsa sakamakon raunin da ya samu. Mahaifinsa kuma tsohon mai horar da shi, Richard Colón, ne ya sanar da rasuwarsa a wani saƙo da ya wallafa a Facebook.
Kafin hatsarin da ya sauya rayuwarsa, Colón na daga cikin fitattun ‘yan damben da ake sa ran za su yi fice a wannan wasa. Ya samu nasarar lashe dambensa 16 a jere, inda ya yi nasarar doke abokan hamayya 13 ta hanyar knockout. Amma a watan Oktoban 2015, yayin wani faɗa da Ba’amurke Terrel Williams a Fairfax, Virginia, Colón ya samu bugun kai da dama a bayan kansa. An kai shi asibiti bayan an gano cewa yana fama da zubar jini a kwakwalwa, lamarin da ya buƙaci a yi masa tiyata cikin gaggawa. Daga bisani ya shafe kwanaki 221 a sume, kuma bai sake iya tafiya ko magana ba.
Raunin Colón ya kuma haifar da sauye-sauye a dokokin damben duniya. A shekarar 2016, Majalisar Damben Duniya (WBC) ta samar da abin da aka kira “Prichard Colón Rule”, wanda ya tanadi tsauraran matakai kan duk wani bugu da aka yi wa ɗan dambe a bayan kai. Bayan faruwar lamarin, iyayen Colón sun kuma shigar da ƙarar neman diyyar dala miliyan 50 a shekarar 2017 kan likitan gefen fili da masu shirya damben da abin ya shafa.
