Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR Birnin Kebbi
Mai martaba sarkin Gwandu Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar ya naɗa tsohon jakadan Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya Farfesa Tijjani Muhammad Bande a matsayin Baraden Besse, uban ƙasar Besse, da ke Jihar Kebbi.
Gwamnan Kebbi mai ci yanzu , Nasir Idris, tare da tsohon gwamnan jihar, Atiku Bagudu, wanda a yanzu shine ministan kasafin kuɗi da tsarin tattalin arziki, da kuma tsohon gwamnan jihar, Jakada Sa’idu Dakingari da kuma tsohon gwamnan jihar, yanzu kuma ɗan majalisar dattijai mai wakiltar Kebbi ta tsakiya, Muhammadu Adamu Alieru, sun halarci wurin bikin naɗin sarautar, wanda aka yi a fadar Abdullahi Fodio da ke Birnin Kebbi, ranar wannan Asabar.
Da yake gudanar da naɗin sarautar, mai martaba sarkin Gwandu, Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar, ya bayyana cewar wannan rana ce da ke cike da farin ciki ga al’ummar masarautar Gwandu, ganin yadda sabon uban ƙasar ya ƙankan da kan sa ga jama’a.
Yace Farfesa Bande bai nuna ɗagawa ba, ya dawo gida domin ya jagoranci jama’arsa a matsayin uban ƙasa, sarautar da ya gada.
Mai Martaba Sarkin Gwandu yana mai cewar a koda-yaushe , Farfesa Bande yana tuntuɓar gida, bai gujema al’ummar sa ba, kuma a yanzu ya dawo cikinsu tsundum bisa jagorancin su da suka amince ma shi ya yi.
Sarki Muhammadu Iliyasu Bashar ya yaba ma Gwamna Nasir Idris dangane da hoɓɓasan da yake yi wurin raya jihar Kebbi.
Mai Martaba Sarkin Gwandu ya yi sharhin cewar kasancewar tsofoffin gwamnoni uku tare da mai-ci yanzu, suka zama su huɗu, a wurin bikin, ya nuna cewar Gwamna Nasir Idris jajirtaccene, kuma mai basiran siyasa wanda ke ƙarfafa haɗinn kai da danƙon zumunci da tafiya bai-daya a jihar Kebbi, a matsayin ginshiƙin zaman lafiya da ci gaban ƙasa.
A jawabin godiya da yayi, sabon Uban Ƙasar Besse, Baraden Besse, Farfesa Tijjani Muhammad Bande, ya bayyana cewar naɗin da aka yi mashi, amana ce mai nauyi aka bashi, kuma ya jaddada cewar zai rike amana da kuma amfanar da al’ummar.
Farfesa Bande, a matsayinsa na khadimin al’umma, ya jaddada mubaya’a da biyayya da goyon baya ga Gwamna Nasir Idris da kuma Mai Martaba Sarkin Gwandu da kuma Majalisar Masarauta.
Yace zai riƙa bada taimakon da al’ummar gundumarsa ke buƙata, sannan kuma ya wanzar da zaman lafiya da tsaro da kuma goyon bayan Gwamnan Jihar Kebbi Nasir Idris ya samu gagarumar nasara a zaɓen da za ayi nan gaba kaɗan.
