Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Gamayyar jam’iyyun siyasa takwas a Jihar Zamfara ta nisanta kanta daga wani taron manema labarai da wasu mambobin gammayyar jam’iyyun siyasa IPAC reshen Jihar da ke ayyana kan su a matsayin shugabannin IPAC a jihar su ka yi.
Da yake jawabi ga manema labarai a yau Asabar a Gusau, Ambasada Adamu Haruna Tsafe, ya ce ƙungiyar ta damu da wannan bayanin, wanda suka lura an yi shi ne da nufin cin zarafi ga manufofi da shirye-shiryen gwamnatin jihar.
Gamayyar ta ƙunshi wakilan jam’iyyun siyasa na AA, NNPP, SDP, ZLP, AAC, LP, YPP da APP.
A cewar Tsafe, taron manema labaran bai wakilci matsayin ‘yan IPAC a Zamfara ba.
Ya bayyana cewa an riga an gabatar da wata takarda da ke ƙalubalantar sahihancin shugabancin IPAC na jihar ga hedikwatar ƙasa ta IPAC da ke Abuja, kuma gamayyar tana jiran amsa.
Gamayyar ta yi zargin cewa an gudanar da zaɓen da ya samar da shugabancin jihar na yanzu ba bisa ƙa’ida ba.
Ta ƙara da cewa, gwargwadon saninta, babu wani shugabanci na IPAC a Jihar Zamfara a halin yanzu.
“Muna so mu bayyana ƙarara cewa jam’iyyun siyasa takwas da suka ƙunshi IPAC ba su san da taron manema labaran ba, kuma muna Allah wadai da shi,” in ji Tsafe.
“Saboda haka, mun nisanta kanmu da abin da ake kira taron manema labarai wanda ba shi da wani dalili illa Banda yunƙurin ɓatawa gwamnatin Jihar kuma a idon duniya,” in ji shi.
Ƙungiyar ta ƙara bayyana duk batutuwan da masu shirya taron suka gabatar a matsayin waɗanda suka samo asali daga rashin adalci da ƙoƙarin ɓata sunan gwamnatin Jihar.
Ƙungiyar ta yi kira ga masu ruwa da tsaki da su bar IPAC ta yi aiki daidai da umarnin ta a matsayin hukumar ba da shawara ga jam’iyyun siyasa, maimakon a maida ta dandalin sukar gwamnatin.
