Abuja na da ’yan fim, amma har yanzu ba ta da masana’anta — Jaruma Steph-Nora Okere

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Abuja na da ’yan fim, daraktoci da masu shirya fina-finai, amma har yanzu birnin bai samu masana’antar fim mai haɗe kanta ba, kamar yadda ake gani a Legas.

Wannan shi ne ra’ayin fitacciyar jaruma kuma mai shirya fina-finai, Steph-Nora Okere, wadda ta ce rashin haɗin kai tsakanin masu ruwa da tsaki na daga cikin abubuwan da ke hana harkar fim a Abuja bunƙasa.

Okere ta bayyana hakan ne yayin da take magana kan buƙatar mayar da Abuja wata cibiyar shirya fina-finai, inda ta ce, duk da yawan ’yan wasan da ke birnin, kowa yana aiki ne da kansa.

A cewarta, akwai ƙungiyoyin ’yan fim daban-daban a Abuja, amma har yanzu ba a samu haɗin kan da zai haɗa su wuri guda domin gina masana’anta ba.

Ta ce irin wannan rashin haɗin kai ya rage saurin bunƙasar harkar fim a Abuja, duk da cewa birnin na da ’yan wasan da za su iya taka rawa wajen gina masana’antar.

Okere ta yi kira ga ƙungiyoyin Actors Guild of Nigeria, Directors Guild of Nigeria da Association of Movie Producers da su haɗa kai wajen samar da wata hanya ta bai ɗaya da za ta taimaka wajen bunƙasa harkar fim a Abuja.

Ta ce hakan zai kuma taimaka wajen jawo hankalin gwamnatin tarayya domin ta ƙara tallafa wa harkar fim a babban birnin ƙasar.

A cewarta, kusancin Abuja da hukumomin gwamnatin tarayya na daga cikin abubuwan da za su iya taimaka wa masana’antar idan aka samu tsarin da zai haɗa masu ruwa da tsaki.

By ukarofi

Leave a Reply