“Ta rasu a ofishin ’yan sanda”: Yadda mutuwar jaruma Temitope Osoba ta sake tayar da hazo

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Sabon iƙirari kan mutuwar jarumar Nollywood, Temitope Osoba, ya sake jawo hankalin jama’a bayan wanda ya ce shi ne wanda za ta aura ya bayyana cewa an sanar da shi mutuwar jarumar ne a wani ofishin ’yan sanda da ke Ikorodu a Legas.

Jaruma Osoba ta rasu tana da shekaru 40, kuma labarin mutuwarta ya fara yaduwa ne a ranar Laraba, 5 ga Agusta.

Jarumar ta taɓa fitowa fili ta bayyana wa jama’a irin gwagwarmayar da ta yi da cutar kansa, bayan an gano tana fama da cutar kuma aka yi mata tiyata.

Saboda haka, bayan rasuwarta, hankalin jama’a ya karkata ne ga tarihin gwagwarmayarta da cutar. Sai dai sabon bayanin da Prophet Itunu Onadeko ya yi ya ƙara buɗe wani sabon babi a cikin lamarin.

Onadeko, wanda ya ce Osoba ce za ta aure shi, ya ce wani mutum da bai san ko wane ne ba ne ya kira shi da misalin ƙarfe 12 na dare, inda ya sanar da shi cewa jarumar ta rasu a wani ofishin ’yan sanda.

Sai dai a cewarsa, shi kansa bai san takamaiman ofishin da ake magana a kai ba.

Haka kuma, a cikin bayanin da aka wallafa, babu wata hujjar hukuma da aka gabatar da za ta tabbatar da cewa jarumar ta rasu a ofishin ’yan sanda. Wannan ya sa sabon bayanin ya kasance abun muhawara da tattaunawa a kafafen sada zumunta, tare da neman gaskiyar lamarin.

Duk da cewa mutane da ya wa sun fi mayar da hankali kan danganta mutuwarta da ciwon sankara wadda ita da kanta ta tabbatar ta yo fama da ita, saidai furucin masoyin nata ya hana hana zuciyoyin masoyan ta da dama hutu, inda suke ganin wajibi ne su bi lamarin don tabbatar da gaskiya. 

By ukarofi

Leave a Reply