
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC, ta sanar da Gwamna mai ci, Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Osun, bayan doke abokin karawarsa na jam’iyyar APC, Bola Oyebamiji.
Baturen zaɓen jihar ne ya sanar da Adeleke na Accord Party a matsayin wanda ya samu nasara a zaɓen a safiyar yau Lahadi bayan kammala zaɓen a jiya Asabar a ƙananan hukumomi 30 na faɗin jihar.
Oyebamiji, wanda shi ne tsohon kwamishinan kuɗin jihar, shi ya zo na biyu, yayin da Najeem Salaam na jam’iyyar ADC ya zo na uku.
Jimillar jam’iyyun siyasa 15 ne suka fafata a zaɓen, inda aka karɓi katin zaɓe 1,906,390, kamar yadda hukumar zaɓe ta bayyana.
Adeleke, wanda ya bar jam’iyyar PDP, wadda a ƙarƙashinta ne ya yi nasara a zaɓen gwamnan jihar na 2022, ya cimma wasu muhimman nasarori a jihar da suka haɗa da ƙoƙarin inganta harkar tattali, samar da ababen more rayuwa, biyan kuɗaɗen fansho, fannin lafiya da samar da sauyin gudanarwar harkar dijital.
Ƙananan hukumomin da Adeleke ya lashe sun haɗa da Oriade, Osogbo, Orolu, Ife ta Tsakiya, Ilesha ta Yamma, Ife ta Arewa, Ede ta Kudu, Ifedayo, Boluwaduro, Iwo da kuma Ifelodun.
A ɗaya gefen kuma, Oyebamiji ya lashe ƙananan hukumomin Ilesha ta Kudu, Boripe, Irepodun, Obokun, da kuma Atakumosa ta Yamma.
Wani rahoton da IntelRegion ta wallafa, ya nuna cewa sakamakon ƙananan hukumomin 30, sun nuna cewa Adeleke ya samu ƙuri’a 511,067, yayin da Oyebamiji ya samu 444,815. Najeem Salaam na ADC, kuwa, ya samu 17,180.
