
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hedikwatar Tsaron Nijeriya DHQ, ta tabbatar da cewa sashen sahfinta na X ya fuskanci kutsen ‘yan damfara, inda ta gargaɗi al’umma da su ƙaurace wa yarda da dukkan wata sanarwa da aka ɗora a kai har sai an shawo kan al’amarin.
Kakakin hedikwatar, Manjo-Janar Sama’ila Uba ne ya sanar da haka a yammacin ranar Asabar a wata takarda da ya fitar.
An ruwaito cewa, an gano haka ne bayan ganin wasu wallafa na tururuwa a shafin, waɗanda suka ƙunshi bayanan harkar kirifto da ba su da alaƙa da sojojin Nijeriya.
Ya ce, shafin da al’amarin ya shafa yana da mabiya sama da 980,000 kuma na ɗauke da sunansa, sahihin bajensa, hotunan sojoji da wasu wallafe-wallafe da aka yi a baya.
A cewar babban jami’in sojin, ana ƙoƙarin shawo kan al’amarin ta sashen tsaron yanar gizo, inda ya ce tuni an riga an ɗauki matakin kariya ta yadda ba za a samu wasu sababbin kutse ba yayin da ake gyaran.
Ya ƙara da cewa, ana kuma ƙoƙarin ganin jagorancin rundunar soji ya karɓi cikakken ikon gudanar da shafin.
Saidai kakakin bai bayyana lokacin da shafin ya soma samun matsalar ba ko bayar da bayani akan waɗanda ke da alhakin kutsen ba. Amma ya tabbatar wa al’umma cewa hedikwatar na gudanar da aikin warwarewa.
