Madugu ya yi wa NFF shaguɓe bayan Falcons ta gaza samun gurbin gasar Kofin Duniya na 2027

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kocin Super Falcons ta Nijeriya, Justine Madugu ya haifar da cece-kuce bayan furta wasu kalamai na shaguɓe jim-kaɗan bayan rashin nasarar da tawagar ta yi a wasan neman gurbin shiga gasar Kofin Duniya na Mata ta 2027.

Waɗannan kalamai sun haifar da alamomin tambaya kan ko kocin yana yi ne da Hukumar kula da Harkokin Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa (NFF) ta bayan fage ko hukumomin gudanar da wasanni ko kuma wasu masu hannu a gudanar da harkokin tawagar.

A cewar Madugu: “kuna tsammanin za ku yi nasara, amma ba ku yi komai ba yayin da wasu suke aiki. Ba haka ake yi ba, ba tsafi ba ne.”

Kalaman na zuwa ne bayan da Super Falcons ta rasa damar shiga gasar Kofin Duniya na Mata a karon fari a tarihin gasar tun fara shi a 1991, lamarin da ya janyo hankalin jama’a.

Duk da cewa Madugun bai bayyana ainihin wanda ko waɗanda yake nufi ba da kalaman nasa, yadda ya furta su ya ba al’umma damar fassarawa ta mabambanta ra’ayoyi.

A ranar Alhamis ne Banyana Banyana ta doke Super Falcons a wasan neman gurbin shiga gasar da ci 2 da 1 bayan Kamaru ta yi waje da ita a gasar Kofin Ƙasashen Afirka na Mata (WAFCON) da ci 1 da 0.

By Babaji