NFF ta fara binciken gazawar Super Falcons ta samun gurbi a gasar Kofin Duniya na 2027

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar kula Harkokin Ƙwallon Ƙafa ta Ƙasa NFF, ta kafa wani kwamiti da ta ɗora wa alhakin binciken ƙwaf akan matsalolin da suka sabbaba wa tawagogin Nijeriya na ƙasa rashin nasara musamman na gazawar Super Falcons samun gurbi a gasar Kofin Duniya na Mata ta 2027.

Wannan mataki na zuwa ne jim-kaɗan da aka yi waje da Falcons a gasar Kofin ƙasashen Afirka (WAFCON) a wasan dab da na kusa da na ƙarshe da ci 1 da nema a hannun Kamaru da kuma ci 2 da 1 a wasan da Banyana Banyana ta Afirka ta Kudu ta doke ta.

Wannan ya nuna cewa a karon farko tawagar Super Falcons ba za ta buga wasan Kofin Duniya ba tun bayan fara shi a shekarar 19991.

A cewar NFF, kwamitin zai yi nazari ne akan dalilan da suka sabbaba rashin nasara ga tawagogin wasan ƙwallon ƙafa na Nijeriya a matakai daban-daban.

Ana sa ran wannan bincike zai gano ababen da suka haifar wa Nijeriya faɗuwa a wasannin ƙasa-da-ƙasa da kuma wuraren da ake da buƙatar ingantawa tare da bayar da shawarwari kan yadda za a kauce wa ire-iren matsalolin a nan gaba.

By Babaji