
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Lahadi, 16 ga watan Agusta, 2026 ne ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal za ta kara da Manchester City a wasan neman lashe kofin ƙasa, wato FA Community Shield na 2026.
Hakan na zuwa ne ƙasa da mako guda da za a buɗe kakar wasannin Premier League ta ƙasar Birtaniya ta 2026/2027.
Arsenal, wadda ta lashe Premier League a kakar da ta gabata, za ta kara da ƙungiyar Man City da ta lashe kofin FA Cup bayan ta doke Chelsea a watan Mayu. Ana buga wasan Community Shield ne dai a tsakanin ƙungiyar da ta lashe Premier League da wadda ta lashe FA Cup.
Wannan zai kasance karon farko da ƙungiyoyin biyu za su haɗu tun bayan wasan Premier League na watan Afrilu, lokacin da Manchester City ta doke Arsenal da ci 2 da 1. Sun kuma kara a wasan karshe na EFL Cup na 2026, inda City ta yi nasara da ci 2 da 0.
Wanda ya yi nasara zai fara kakar da kofin babbar gasa ta cikin gida. Sai dai tarihi ya nuna cewa lashe Community Shield ba lallai ne ya tabbatar da lashe Premier League ba, domin tun daga 1992, kungiyoyi takwas ne kawai suka samu nasarar lashe kofunan biyu a kakar wasa guda.
